Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojojin Saman Najeriya Ta Ceto Yan China 7 Daga Masu Garkuwa


Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su
Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Yayin wani farmakin da sojoji na musamman daga sashi na 171 da mayakan saman Najeriya, su ka kaddamar kan wani sansanin barayin daji, an sami nasarar ceto wasu yan kasar China 7 da ake garkuwa da su.

Kakakin Hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gwabket ya shaidawa muryar Amurka cewa, yan kasar Chinan suna aikin hakar ma'adinai a yankin Shiroro, lokacin da masu garkuwa da mutane su ka sace su tun watanni shida da suka wuce, inda aka tafi da su dajin birnin gwari da ake kira Gwaska kusa da Kamfani Doka a cikin jihar kaduna.

Da yake karin haske kan yadda aka bi aka kubutar da yan kasar China, kakakin sojojin saman Najeriyar ya ce dama ana zargin akwai mutane marasa gaskiya a wannan wuri, inda da Asubahi aka shirya wani tsararren farmaki cikin kwarewa da kazar kazar.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su
Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Sojoji na musamman da ga mayakan saman Najeriya sun afkawa wurin da ake garkuwa da mutane, inda yan bindigar su ka bude wa sojojin wuta, nan take suma dakarun suka maida mummunan martini a cewarsu.

Bayan da masu garkuwar su ka tabbatar da sojojin a shirye suka je, hakan ya sa suka zubar da makamansu suka arce, tare da barin mutanen da suke garkuwar da su a baya.

Daga nan an kwashe ‘yan kasar Chinan zuwa sansanin mayakan saman dake Birnion Gwari, kafin daga baya a wuce da su zuwa Babban Asibitin sojojin sama dake Kaduna, domin duba lafiyarsu.

Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su
Yan Kasar China Da Sojojin Najeriya suka ceto bayan anyi garkuwa da su

Air commodore Gwabket ya nanata kudirin Rundunar sojojin saman Najeriya, nayin aiki kafada da kafada da sauran jami'an tsaro wajen ci gaba da kare dukiya da rayukan yan Najeriya da sauran mazauna kasar.

Saurari rahotan cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG