A gefe guda kuma suma tsagerun kudu maso gabas dake neman ballewa daga Najeriya ke cewa ba za su bari a gudanar da zaben a yankunansu ba''
To amma Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Tsaron Najeriya Janaral Lucky Irabor ya jagoranci wani taron gaggawa da baki dayan manyan Hafsoshin sojoji da sauran shugabannin hukumomin tsaron kasar a wani bangare na tabbatar da samar da cikakken tsaro yayin babban zabe na kasa da za gudanar a kasar
Taron na zuwane a daidai lokacin da mayakan Boko Haram suka saki wani faifan Video da a ciki suke barazanar kawo cikas yayin zaben, kana a gefe daya kuma suma Tsagerun yankin kudu maso gabas dake rajin ballewa daga Najeriyar sun sha alwashin kawo cikas a zaben.
Amma Babban Hafsan Hafsoshin ya jaddada cewa baki dayan jami''an tsaron kasar sun shirya tsaf don fuskantar duk wani mutum ko kungiya dake son gwada karfin hukuma, yana gargadinsu da su yi wa kansu kiyamullaili ko kuma su yaba wa aya zaki.
Janaral Lucky Irabor ya ce sun yi nazarin jadawalin tsarin tsaron kasar da ma halin da kasar take ciki inda ya jaddada cewa jami'an tsaro shirye suke su samar da tsaro da kuma kare masu jefa kuri'a don gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali da lumana.
Cikin manyan kusoshin tsaron da suka halarci taron akwai manyan hafsoshin sojojin kasa, ruwa da na sama, da babban sufeton yansanda na kasa da kuma shugabannin hukumomin tsaro na kasa na DSS, DIA da NIA.
A cewar masanin tsaro Manjo Bashir Galma mai ritaya wannan gagarumin taron fa na nuna irin namijin tsari da akai don kawo tsaro a wannan zabe inda yake shawartar duk wadanda ke da wani shirin boye na wargaza zaben da su sake tunani.
Shi ma shugaban hukumar gangamin wayar da kan jama'a na Najeriya Dr. Garba Abari ya nemi masu kada kuri'a da su fito don yin zabe, sannan su kiyayi tada fitina ko sayar da kuri'a, abin da yace tamkar sayar da 'yancin su ne.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina: