Biyo bayan ayyana wasu jagororin ‘yan bindiga 19 da rundunar tsaron Najeriya ta yi a matsayin wadanda sojoji ke nema ruwa a jallo, kawararru a kasar da wasu jama’ar yankin arewa maso yammaci, na ci gaba da bayyana ra’ayoyi mabanbanta.
Cikin jerin jagororin ‘yan bindigar da hedkwatar tsaron Najeriya ta wallafa hotuna da sunayensu, guda 10 ‘yan asalin jihar Zamfara ne, takwas mazauna jihar sai daya daga Sokoto.
Cikin sanarwar da ya sanyawa hannu, kakakin hedkwatar rundunar tsaron Najeriya, Manjo Janar Jimmy Akpor ya ce, akwai tukwicin Naira miliyan biyar da aka sanya ga duk wanda ya ba da bayanan da za su kai ga kama daya daga cikin ‘yan bindigar.
Su dai wadannan jerin 'yahn bindiga, su ne kan gaba, wajen jagorantar gungun 'yan ta'adda da ke tafka aika-aika a jihohin arewa maso yammacin Najeriya.
Sai dai ‘yan asalin yankin da abin ya shafa kai tsaye na kaffa-kaffa kan wannan sabon mataki na rundunar tsaron kasar.
Mai sharhi kan al'amuran tsaro, Farfesa muhammad Tukur Baba Dan Iyan Mutum biyu, ya nuna matukar mamaki da wannan mataki da sojoji suka dauka, inda yake cewa, kowa ya san inda ‘yan bindigar nan suke ciki har da jami’ai.
Farfesan ya kuma ce, daya daga cikin 'yan bindigar da ake nema, har sarautar gargajiya aka ba shi a jihar Zamfara a gaban jami'an gwamnati da na tsaro, yana mai cewa in har da gaske ake yi, da za a iya kama shi.
Amma Farfesa Tukur Dan Baba, ya yi kira ga jama'a da ba su jami'an tsaron goyon baya.
Wasu daga cikin ‘yan yankin na arewa maso yammacin Najeriya sun shaidawa Muryar Amurka cewa, zai yi wuya su ba da goyon baya ganin a baya sun sha yin hakan amma daga baya ‘yan ta’addan su zo su auka masu, suna ikirarin cewa babu dan ta’addan da gwamnati da jimi'an tsaro ba su san inda suke ba.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja: