“Duk wanda ya kai shekara daya har zuwa shekara 100 zai samu wannan magani.”
Al’umar Kiristoci a jamhuriyar Nijer sun dauki alwashin yin addu'o'i domin samun zaman lafiya da kawo karshen karshen matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta a kowane gefe.
Gwamnan Jihar Tahoua ya kai ziyara a babban asibitin birnin Jaha, domin gaida sojojin jamhuriyar Nijar da wadansu mahara da a ke zaton sun tsallako ne daga kasar Mali su ka jikkata a yankin Tilliya, a wani kazamin arangama.
Wadansu mutane da suka kai 50, dauke da manyan bindigogi ne, in ji mutanen garin Kwandamo a cikin karamar hukumar mulkin Illela ta Jihar Sokoto, da ke kan iyaka da birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar suka kai harin.
An yi hawan idin babbar sallah a yau Talata a dukkan fadin kasar Jamhuriyar Nijar inda shugaban kasar Bazoum Mohamed da sauran mukarraban gwamnati da suka raka shi wurin wannan hawan idin babbar sallar a babban massalacin Kaddafi na babban Birnin Yamai.
Hukumomin jamhuriyar Nijer tarevda masu hannu da shuni dake tallafawa kasar a fannin kiyyon lafiya, suna shirya gangamin allurar rigakafin cutar shan'inna a jahohin Maradi - Tahoua da Zinder.
Daya daga cikin sarakunan Musulmi 4 Ali Zaki na Katsina Maradi ya rasu kamar yadda hukumomin jihar Maradi suka tabbatar wa manema labarai.
Dubun wadansu mahara masu garkuwa da mutane ta cika a garin Garu a karamar hukumar mulkin Illela ta jihar Sokoto da ke iyaka da Birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar, yayin da wadansu suka kashe mutun guda a Araba dake da tazarar kilomita 2 da birni N'Konni.
Yau Laraba al’umomin Jamhuriyar Nijar suka yi karamar sallah biyo bayan sanar da ganin watan Shawwal, wanda ya kawo karshen watan Ramadan.
Majalisar koli ta addinin islamaa Nijar ta bayyana ganin jinjirin watan Shawwal dake nuna an kamalla azumin Ramadan na wannan shekara.
Yan ta'adda da ake kyautata zaton sun bullo daga kasar Mali ne, sun yi wa askarawan Nijar da ke sintirin tsaro da wanzar da zaman lafiya a yankin Tillia dake arewacin jahar Tahoua kwatan bauna, inda suka kashe soja 16
‘Yan bindiga sun yi barin wuta a garin Tunga da ke karamar hukumar Illela a jihar Sokoto, lamarin da ya sa mazauna garin gudun tsira da rayukansu zuwa makwabtan garuruwa.
Bayan binciken da gwamnatin jamhuriyar Nijer ta gudanar, ta ce ‘yan ta'adda da suka fito daga kasar Mali sun kai hare hare a cikin garuruwa da dama da wata tunga a cikin gundumar Tilliya ta jihar Tahoua inda su ka kashe mutane 137 wasu da dama kuma suka jikata.
Wadansu 'yan bindiga da a ke kyautata zaton masu tsattsauran ra'ayin addini ne da suka kutso daga kasar Mali, sun abka wa garuruwa 2 na gundumar Tilliya a cikin jahar Tahoua jamhuriyar Nijar, su ka kashe mutane 54.
Kotun kolin tsarin mulkin kasa ke da hurumin tabbatar da an kammala zabe, ba wani dan siyasa ba.
Rundunar ‘yan sanda ta gundumar tsibirin Maradi a Jamhuriyar Nijar, ta cafke wadansu mutane masu fashi da makami, da suka hada da maza 3 da mata 2.
Iyalin wani mutum da masu garkuwa da mutane suka kashe a yankin Amarawa na Jamhuriyar Nijar, sun yi kira ga 'yan bindigar da ba su gawar dan uwansu bayan da suka samu labarin cewa an kashe shi.
An gargadi kamfanonin wayar sadarwa a jamhuriyar Nijar, da kada su yanke wa jama'a damar amfani da yanar gizo a bisa dalilin da ba su ne su ka yi sanadi ba.
Matan nan da ‘yan bindiga suka abkawa cikin gidansu kuma suka yi garkuwa da su a kan iyakar Nijar da Najeriya sun kubuta bayan an biya kudaden fansa.
Wasu 'yan fashi ne suka yi awon gaba da matan wani bawan Allah a kauyen Kalmalao.
Domin Kari