Biyo bayan wani lamari mai cike da ban tsoro, bayan afkawar da maharan suka yi wa jama'ar garin Amarawa a kan iyakar Nijar da Najeriya, mako guda da ya gabata, al'umar Fulani da ke yankin sun fara ficewa daga garuruwansu domin tsira da rayukan su.
Hakan ya biyo bayan fushi da matasan Amarawa suka yi inda suka far wa al'umar Fulanin.
Karin bayani akan: Nijar, Fulanin, Amarawa, Nigeria, da Najeriya.
Sai dai hukumomi sun yi kira ga matasa da kada su sake taba kowa, kuma su bar Fulanin su ci gaba da harkokin su na yau da kullum, a cewar Alhaji Dan Jumma Amarawa.
Bayan mutun 12 da suka mutu a harin ranar Lahadi, har yanzu ba'a gano inda gawar na 13 da jama'a suka tafi ceto ba, wadanda 'yan ta'adda suka kashe su, abin da ke kara fusata jama'ar garin, inda suka yi kira ga masu yin garkuwa din da su ba su gawar mutumin.
Kwanciyar hankali ta fara samuwa da rana, sai dai da dare ya karato, dubban mutane ke kwarara zuwa Nijar domin kwana a matakin neman mafaka da tsira da rayukansu.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako a cikin sauti.