A lokacin da ta ke bayyanawa ‘yan jarida yadda al’amarin ya faru, Shugabar rundunar ‘yan sanda ta tsibirin Maradi, Rahila Alfa, ta ce barayin sun tafi da mai dabbobin har wannan ruga, sai ya kirawo ‘yan sanda wanda suka kai dauki cikin hanzari.
Shugabar rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa a lokacin da aka kama barayin shanun, an samu bingigogi kira AK-47 guda 2 da adda guda 3 da takobi guda, da kwari guda 2, da baka guda, da dabbobi 172 a wata rugga da ke kilomita 7 da garin tsibirin Maradi da ake cewa Doguwar Kurya, sai dai shugaban ‘yan fashin ya diba cikin ta kare.
Karin bayani akan: gwamnan jihar Maradi Zakari, Nigeria, da Najeriya.
Yi kira da wadanda suke taimakawa jami’an 'yan sanda da bayanai da su cigaba da kokarin da suke yi.
A na shi bayanin, gwamnan jihar Maradi Zakari Umaru ya shaidawa manema labarai cewa, wannan abun bakin ciki ne iftila’in da ke can bakin iyaka yana tahowa yanzu har ya kawo cikin birane.
Ya ce da suna zaton masu yi musu barnan daga waje suke ketarowa suna musu barna suna komawa. Yanzu nasu ne su ke barnan saboda akwai mutane da suke fada musu cewa ku yi hankali yau jami’an tsaro suna waje kaza. Ya kuma bayyana cewa, gwamnati tana iya kokarinta kuma ta zuba jami’an tsaro da yawa a kan iyaka.
shi ma a hirar sa da Muryar Amurka, Sultant na Gobir, Alhaji Abdu Bala Maradi da Shugabn rundunonin ‘yan sanda na jihar Maradi Amadu Mossi sun jinjina ta musaman ga ‘yan sandan tsibirin Maradi, tare da kira ga al'umma su ba ‘yan sanda hadin kai da labaru don su kare al'ummar Nijar.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako: