Sultan Ali Zaki ya kasance daya daga cikin Sultan 4 ko sarkin Musulmi na Nijar, bayan Sultan na Zinder, Agadez da Dosso.
Kuma yana mulkin masarautar Katsina Maradi da ke kasancewa cibiyar tattalen arzikin Jamhuriyar Nijar kuma jiha mafi yawan al'umma a kasar.
Muryar Amurka ta tuntubi Alhaji Salisu Issa, wani Dan jarida dake Maradi ya ce Sarkin ya dade yana jinya kafin Allah ya yi masa rasuwa.
Ita dai masarautar Maradi na kasancewa daya daga cikin manyan masarautun kasar da ta yi suna sosai a karni na 18 a lokacin mulkin Bawa Jan Gorzo.
Har izuwa yanzu, bayan kira da sanar da manema labarai da rasuwar sultan na Maradi Ali Zaki da ma'aikatar gwamnan jihar Maradi ta yi, ba wata sanarwa da hukumomi na jihar ko na kasar suka yi game da wannan rashin da kasar tayi.
Saurari cikakken rahaton cikin sauti: