Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka inda ya ce sabanin hakan zai iya haifar da cikas ga tsarin dimokradiyya.
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ta ASUU ta tsawaita yajin aikin da ta fara watanni 3 da suka gabata zuwa watan Agusta, bisa dalilai masu alaka da halin ko-in-kula da ta ce gwamnatin Najeriya na nunawa.
Kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu na jigilan fasinjoji a Najeriya sun dakatar da yajin aikin da suka shirya farawa yau, sakamakon shiga tsakani da gwamnatin kasar ta yi.
A yayin da Najeriya ke cigaba da fama da matsalar wutar lantarki, Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana cewa zata cigaba da aiki tare da taimakawa kasar wajen shawo kan matsalar da taki ci taki cinyewa.
Kungiyoyin mata sun gana da babban Sakataren Majalisar Dinkin duniya Antonio Gutteresshi tare da kai koke don ya taimaka wajen tabbatar da rage matsalolin da mata ke fuskanta a kasar ta hanyar bada tallafi da kuma farkar da gwamnatin kasar.
Ma’aikatan majalisar 23 ne suka rasa rayukansu, wasu 116 kuma suka jikkata a lokacin da wani bam ya tashi a ofishin majalisar da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Masana kundin tsarin mulki sun ce ya kamata gwamanti ta yi duk mai yiyuwa wajen kubutar da metanen da ke hannun yan bindiga.
A wani al'amari mai dada jaddada aniyar Mataimakin Shugaban Najeriya, Yomi Osunbajo, ta tsayawa takara, ya ce muddin bai bukaci tsayawa takarar ba, tamkar cin amanar 'yan Najeriya ya yi. Ma'ana, wajibi ne ma a gare shi ya nemi tsayawa takarar.
Ga dukkan alamu, har yanzu rigimar da Shugaban Kotun Ma'aikata, Danlada Umar, ya shiga, ta zargin cin zarafi ba ta kare ba. Hasalima, kusan ta dada kasaita bayan da wata kotu ta ce akwai hurumin bincikarsa.
A yayin da ‘yan kasa ciki har da manoma ke dakon daminar shekarar 2022 hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya wato NIMET ta ce za’a fara daminar bana a watan Mayu kuma zata kusan yin daidai da ta bara.
Tsarin fara sayen tikitin jirgin saman fita waje da kudin dala da aka sanar cewa wasu kamfanonin jiragen sama zasu yi ya fara aiki a ranar 19 ga watan Afrilun nan da muke ciki.
A daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben fidda gwanin manyan jam’iyyun siyasar Najeriya biyu wato APC da PDP, wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC sun yi kira ga shugabannin jam’iyyar su kwatanta adalci.
Har yanzu dai ‘yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da yan ta’ada suka yi garkuwa da su bayan tarwatsa wani bangaren jirgin da bam na neman gwamnatin kasar ta dube su da idon rahama.
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya maida martani kan cece-ku-cen da ya biyo bayan rabawa sarakunan gargajiya a jihar motoci da kuma alakantan sayen motocin da zunzurutun kudin da aka kiyasta cewa ya kai biliyoyin nairori.
Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina kuma shugaban kwamitin tantance 'yan takara da suka tsaya neman mukamai daban-daban a karkashin jam’iyyarsu ta APC da ta ke gudanar da babban taronta a yau, 26 ga watan Maris, ya bayyana cewa kwamitinsa ya sami nasarar tantance 'yan takara 189.
Wasu matasa da masana kundin tsarin mulki na ganin cewa ya dace a cire bayanin addinni da asalin jihar da mutum ya fito a takardar bayanin mai neman aiki wato CV don rage matsalolin kabilanci a kasar.
Domin Kari