Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIMET Ta Yi Hasashen Kamawar Damunar 2022 A Watan Mayu


Taron NIMET
Taron NIMET

A yayin da ‘yan kasa ciki har da manoma ke dakon daminar shekarar 2022 hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta Najeriya wato NIMET ta ce za’a fara daminar bana a watan Mayu kuma zata kusan yin daidai da ta bara.

Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin taron hasashen yanayi karkashin tsarin sashen Sudan da Sahel da ya kunshi kasashe 17 a Abuja baboon birnin tarayyar Najeriya.

Taron NIMET
Taron NIMET

Ana sa ran daminar shekarar 2022 a kasashen yankin Sahel da Sudan ciki har da Najeriya ta kan-kama a watan Mayun mai zuwa a mizanin tsaka-tsaki kamar yadda alkaluman dandalin hasashen yanayi kasashen 17 karkashin shirin PRESAS na lokacin daminar wannan shekarar ya yi nuni.

Taron NIMET
Taron NIMET

Shugaban hukumar NIMET Farfesa Mansur Bako Matazu wanda Mailadi Yusuf ya wakilta ya ce makasudin taron kasashe goma sha bakwai shine bayyana yanayin da daminar bana zata kasance.

Taron NIMET
Taron NIMET

Mai bincike a kan yanayi a bangaren aikin noma na NIMET James Adamu Jampi, ya yi karin bayani kan yiyuwar samun Fari a wannan shekarar.

Dangane kuma da tanadi ake a birnin tarayyar Abuja don tunkarar daminar ta bana musamman ta fuskar daukan matakan shawo kan matsaloli masu alaka da ambaliyar ruwa, babban daraktar hukumar bada agajin gaggawa ta birnin Abuja wato FEMA, Abass Idris ya ce an tashi tsaye don duba kan ayyukan kamar yadda suka kamata kafin damuna ta kama.

Taron NIMET
Taron NIMET

A shekarar 2021 an sami ambaliyar ruwa a jihohin Kebbi, Legas, babban birnin tarayya da ma wasu jihohin kasar, lamarin da ya janyo kiraye-kiraye daga manoma da sauran masu ruwa da tsaki da su rika daukan matakan da suka dace akan lokacin.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

NIMET Tayi Hasashen Kamawar Damunar 2022 A Watan Mayu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

XS
SM
MD
LG