Suna bukatar ta kubutar da yan uwan nasu dake cikin mawuyacin hali a hannun 'yan bindigar da suka ce ba su da magana da kowa sai gwamnatin kasar.
‘Yan uwan mutanen dake hannun ‘yan ta’adan dai sun yi tattaki zuwa hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya dake babban birnin tarayyar kasar Abuja a ranar Alhamis wanda ke kasance kwanaki na 17 da yan uwansu ke tsare a cikin daji.
Wannan tattakin dai na zuwa ne kasa da kwanaki uku da wasu daga cikin yan uwan mutanen dake tsare a daji suka ba da wa’adin sa’o’i 72 su kubutar musu da ‘yan uwan nasu a wata ganawa da manema labarai.
Aliyu Mahmud ya ce shi ne dan'uwan wata mata dake dauke da cikin wata bakwai wacce ke tsare a hannun 'yan bindigar a daji.
Ya ce yanzu haka suna cikin tashin hankali fiye da misali kuma sun dangana ne da Allah.
A yayın da wasu ‘yan uwa ga wadanda aka yi Garkuwa da su a cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ma wasu ‘yan Najeriya ke ganin gazawar gwamnati wajen yaki da matsalolin tsaro a kasar, tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa ba shakka jama'a suna ganin gazawa gwamnatu amma gaskiyar maganan ita ce aiki ya yi wa masu tsare kasar yawa.
Duk da cewa mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo, ya ziyarci Kaduna don nuna alhini ga lamarin da ya rutsa da darurruwan mutane a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, iyalan mutanen da aka sace din da ma wadanda suka rasa ransu a yayın harin sun ce alhakin kare rayuka da dukiyoyin mutane na wuyan gwamnati ne.
Sun kara da cewa suna cikin bakin ciki a game da yadda hukumomi ke ci gaba da nuna halin ko in kula da ganin an sako ‘yan uwansu.
Hukumomin Najeriya dai sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun kare rayuka da tabbatar da tsaro a kasar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: