Shugaban kungiyar kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu na Najeriya kuma mai kamfanın jiragen saman jigilan fasinjoji na Azman, Dakta Abdulmunaf Yunusa Sarina, ne ya bayyana wannan matakin janye yajin aiki da suka shirya farawa a hirar shi da Murayar Amurka.
Dakta Abdulmunaf dai ya ce sun dauki matakin ne sakamakon tuntuba da ta samu daga gwamnatin tarayyar kasar da ta nemi a ba ta wa’adin sa’o’i 48 ta gana da masu ruwa da tsaki a fannin sufurin jiragen saman kasar domin daukan matakan da suka dace.
Kamfanonin jiragen saman masu zaman kansu sun dauki wannan matakin ne sakamakon yanayin tsadar man tafiyar da harkokin nasu wanda ake saya sama da naira 700 sabanin kasa da naira 200 da aka saba saya a da in ji Dakta AbdulMunaf.
A baya dai sai da kamfanin NNPC ya shiga tsakanin kamfanonin jiragen saman kasar da dilallan man da ake amfini da shi wajen tafiyar da harkokin sufurin jiragen saman inda aka tsaida farashin man a kan naira 500, sai dai daga bisani farashin ya ci gaba da tashi kamar yadda shugaban kamfanin jirgin saman Airpeace ya bayyana a baya.
Kafin daukan wannan mataki na fara yajin aikin gamagari da kamfanonin jiragen saman kasar masu zaman kansu suka tsayar farashin tikitin jirgin sama ya fara ne daga naira dubu 50 zuwa sama lamarin da fasinjoji ke korafi a kai.
Sai dai shugaban kamfanin jirgin saman Azman, Dakta AbdulMunaf, ya ce ba wai ba zasu Iya ci gaba da aikin su ba amma fasinja zai wahala har in farashin kowanne tikiti ya koma dubu 120.
Malam Shamsudeen Ishaq wanda ya saba zirga-zirgar kasuwancinsa tsakanin Legas, Kano da Abuja ya bayyana farin ciki matuka da labarin janye yajin aikin da kamfanonin jiragen saman kasar suka yi yana mai cewa, ya shiga halin ha’ula’i bayan samun kabarın za’a shi yajin aikin a ranar juma’ar da ta gabata.
Ita ma yar kasuwa Aisha Tukur mai zirga-zirgar kasuwanci tsakanin Abuja zuwa Kano sarin kaya ta ce ta yi farin ciki matuka da kamfanonin suka janye yajin aikin tana mai cewa ta shiga rudani kan yadda zata yi tafiya Kano da mota ta je dauko kayan da ta bada oda da ya kamata ta gani da idonta kafin a kawo wa wadanda ke da bukata.
A ranar juma'ar data gabata ne kamfanonin jiragen saman kasuwar kasar da suka hada da Air Peace, Ibom Air, Max Air, Arik Air, United Nigeria, Azman da wasu karin kamfanonin jiragen sama 3 suka fitar da sanarwar cewa zasu tsunduma yajin aikin gamagari daga ranar litinin 9 ga watan Mayun sakamakon tsadar man tafiyar da harkokinsu.
A ranar lahadi ne kamfanin Ibom air ya sanar da cewa ya fice daga cikin kamfanonin jiragen saman da suka shirya fara yajin aikin lamarin da shugaban Azman ya ce bai sa su yi kasa a gwiwa ba, bisa la'akari da cewa Ibom air wani bangaren gwamnati ne kuma zai iya daukan matakan da ya so.
Abun jira a gani shi ne ko za’a sami cimma matsaya mai dorewa kan farashin man na jiragen sama takanın dilallan man, kamfanonin jiragen saman da sauran masu ruwa da tsaki.