A wannan makon, shirin lafiyarmu zai yi nazari kan yanayi ko sosawar zuciya da masoya wasanni daban-daban ke shiga ko samu da kuma abinda zai haifar musu.
Yadda Cutar Dajin Gaban Namiji Ko Kuma Prostrate Cancer A Turance Ke Shafar Maza A Nahiyar Afrika
Bankin CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulansu a game da tsarin saboda an yi ne don ci gaban kasa, ba wai don kuntatawa al’umma ba.
Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyana cewa, ya gabatar da sabon tsarin daukar kudi ne da nufin rage tsabar kudin da ke hannun jama'a.
Jakadan Najeriya a kasar Rasha, Farfesa Abdullahi Yibaikwal Shehu, ya ja hankalin sabbin daliban Najeriya da suka iso kasar Rasha a bisa tsarin tallafin karatu tsakanin Najeriya da kasar Rasha na shekarar 2022 zuwa 2023.
A wannan makon, shirin Lafiyarmu zai maida hankali ne a kan ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki wato AIDS wacce aka ware 1 ga watan Disamba don wayar da kan al’umma a kan cutar Musamman yadda kwararru suka ce ana ci gaba da samun rashin daidaito a yaki da cutar.
A daidai lokacin da ake ganin kamata ya yi Najeriya ta kara himma wajen aikin cimma kudurorin nan 17 na raya kasashe wato SDGs na MDD don kawo karshen talauci baya ga tabbatar da wadata ga kowa da kowa, Najeriyar da ma MDD sun rattaba hannu a kan tsarin hadin gwiwa na shekarar 2023 zuwa 2027.
“Yanzu mun saka na’urar da za mu iya ganin jirgin nan daga tashinsa har isar shi. Akwai na’urori da za sui ya gaya mana ko akwai matsala.”
Sama da watanni 7 da dakatar da zirga zirga tsakanin Abuja da Kaduna, sakamakon harin 'yan ta’adda, Ma’aikatar sufuri da hukumar NRC sun gudanar da jigila ta gwaji daga Abuja zuwa Kaduna don da duba matakan tsaro da gwamnati ta dauka a kan hanyar dai sauransu.
A wannan makon, shirin Lafiyarmu zai maida hankali ne kan raunukan da ake samu a wasanni da kuma yadda za’a iya kare Kai daga samun raunukan yayin da aka fara gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a kasar Qatar.
Babban kwamandan rundunar tsaron sibil defence, Farfesa Ahmad Abubakar Audi, ya ce mata sun fi mayarda hankali a kan aiki idan aka basu dama shi yasa hukumar NSCDC ta kafa punduna ta musamman don taimakawa matan da su suka fi tagayyara idan aka fuskanci wani tashin hankali.
Tsarin narkewar abinci a ciki ya haɗa da sashin hanji ko gastrointestinal ko abunda ake kira GI, cikin mutum, ƙanana da manyan hanji, da gabobi kamar su hanta, dake taka muhimmiyar rawa wajen mai da abincin da muke ci ya zama mai amfani ga jiki.
Hakan na faruwa ne yayin da shi ma Kanu ya ki yarda ya bayyana a gaban kotu saboda yana kulabalantar kin bin umarnin kotun daukaka kara da hukumomi suka yi
Duk da cewa Naira ta fara farfadowa daga faduwa da ta yi a cikin makonnin 2 da suka gabata har ta kai ga naira 910 a bisa dala 1 wanda yanzu an sami farfadowa da kaso 20.8, naira ta koma 720 a bisa kowacce dala 1, masana tattalin arziki na ganin salon da aka dauka ke karya lagon darajar Naira din.
Masana na hasashen cewa sauyin yanayi zai ƙara yin barazana ga lafiyar ɗan adam, musamman a cikin al’umomi masu karamin karfi.
Wata babbar kotun birnin tarayya ta yankewa Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC hukuncin zama a gidan kaso sabili da gazawar hukumarsa na kin bin umarnin kotu na baya.
A Najeriya, masana sun kiyasta cewa mata dubu 17 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon kamuwa da cutar sankara ko kansar mama saboda yadda akasarin masu fama da cutar ba sa zuwa asibiti a kan lokaci.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tallafin kasa da kasa don yaki da barkewar cutar kwalara a tsakanin 'yan gudun hijira.
Masu ruwa da tsaki da suka hada da wakilan al’umma, masu fashin baki kan al’amuran yau da kullum da lauyoyi sun bayyana cewa, har yanzu Najeriya ba ta kai ga lokacin kafa ‘yan sandan jihohi ba la’akari da yadda ake zargin gwamnonin jihohi da juya kwamishinonin ‘yan sanda a jihohinsu.
Matsalar karancin man fetur ta kara ta’azarra a sassa daban-daban na Najeriya, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa da direbobin motocin kasuwa shafe sa’o’i ko kuma kwana a gidajen mai a lokacin da suke fafutukar nema don gudanar da al’amuransu na yau da kullum
Domin Kari