ABUJA, NIGERIA - Hakan na zuwa ne kasa da kwanaki 10 da majalisun tarayyar Najeriya suka sanar da cewa majalisun jihohi 11 ne kawai suka amince da kudurorin gyare-gyare a kundin tsarin mulkin kasar bayan watanni 6 da aika musu don neman amincewarsu.
‘Yan majalisun tarayya da na jihohi, masu bibiyar al’amuran yau da kullum, iyaye mata da ma lauyoyi sun bayyana hakan ne a yayin taron zuren VOA da ya gudana a birnin tarayya Abuja suna masu cewa ganin yadda Najeriya ba ta gama tsayuwa a kan tsarin mulkin dimokuradiyya ba ta yadda za a ce lokaci ya yi na kafa ‘yan sandan jihohi, kamata ya yi a guje wa abun da ka je ya dawo.
Mahalarta taron dai sun yi ta bayyana rashin jin dadinsu a kan yadda majalisun jihohi 25 suka ki daukar mataki a kan gyare-gyaren da kwamitin majalisun tarayya suka tura musu a watanni 6 da suka gabata inda suka gindaya wasu sharudda kamar bukatar a sanya batun kafa ‘yan sandan jihohi a matsayın wajibci.
Aliyu Sabi Abdullahi, sanata mai wakiltar mazabar jihar Neja ta arewa a tarayyar Najeriya, ya bayyana cewa kusan kullum al’umma na bukatar a yi musu bayani a kan abubuwan dake tafe a kasa tare da cewa ana bukatar kafa ‘yan sandan jihohi sai dai lokacin hakan bai yi ba.
A nasa bangare, fitaccen lauya barista Mainasara Kogo ya yaba da kokarin ‘yan majalisun tarayya a game da aikin gyara kundin tsarin mulkin kasar, saidai baya ga hakan ya soke su a game da mayar da batun gyarar kundin tsarin mulkin kamar wata al’ada a kowanne zauren majalisa suna fito da zunzurutun kudi kuma daga karshe ba tare da yin nasara a gyarar da ya kamata a yi ba.
Idan Ana iya tunawa, kwamitocin majlisun tarayyar Najeriya da suka duba batun gyara kundin tsarin mulkin sun mikawa majalisun jihohin kasar 36 takardar gyare-gyaren ne a watannin 6 da suka gabata don samun amincewarsu kafin sanar da cewa jihohi 11 kawai ne suka jefa kuri’a a kan batun gyarar.
Jihohi 11 da suka dauki mataki a kan batun yin gyara a kundin tsarin mulkin dai sun hada da Abia, Akwa-Ibom, Anambra, Delta, Edo, Kaduna, Katsina, Kogi, Legas, Ogun da Osun kamar yadda mataimakin shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitocin majalisun, Sanata Ovie Omo-Agege, ya bayyana.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf: