Sabon shiga a harkokin siyasa Mohamed Hussein Roble ya zama Firaiministan Somaliya jiya Laraba bayan da daukacin ‘yan majalisar dokokin kasar suka amince da nadinsa.
Shugaban Somaliya, Mohamed Abdullahi Mohamed ya halarci zaman majalisar a lokacin da dukkan mambobinta 215 suka kada kuri’unsu don nuna goyon baya ga wanda ya nada.
Sabon firai minister Roble ya yi alkawarin samar da gwamnati mai inganci da za ta magance wasu manyan matsalolin da kasar ke fuskanta, ciki har da batun yin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki cikin adalci.
A watan Yuli ‘yan majalisa suka kada kuri’ar yanke-kauna akan tsohon firai minista Hassan Ali Khaire da Roble ya gada saboda gazawar da ya nuna wajen shata turbar da za a bi wajen gudanar da zaben da ke tafe a watan Fabrairun badi.
Facebook Forum