An mayar da Sanusi Muhammadu a matsayin Sarkin Kano bayan ya karbi takardar nadinsa daga Gwamna Abba Yusuf ranar Juma'a.
Mai shari’a Mohammed Liman ne ya mika wannan umarnin ga gwamnatin ta Kano.
A ranar Alhamis ne aka rantsar da Janar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya jagoranci mulkin sojan Chadi na tsawon shekaru uku, a matsayin shugaban kasa.
Bsaïs da Zeghidi sun musanta zargin. Dukkansu sun ce suna gudanar da ayyukansu ne kawai, wajen nazari da sharhi kan ci gaban siyasa da tattalin arziki a Tunisiya.
Kasar Benin ta toshe mashigar kan iyaka da Nijar ta ratsa tsakanin makwabta, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Alhamis, a wani tashin hankali da ya barke tun bayan da sojoji suka kwace mulki a Yamai a watan Yulin da ya gabata.
Firaministan Spain Pedro Sanchez ya ce an dauki matakin ne da nufin kara kaimi wajen ganin an tsagaita bude wuta a yakin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza.
Ministan Sadarwa na Isra'ila Shlomo Karhi ya ce ya soke umarnin bayan da ya zargi kamfanin dillancin labarai na AP da saba sabuwar dokar hana bayar da hotunan Gaza zuwa ga tashar Al Jazeera da ke Qatar.
Jirgin Boeing 777-300ER, mai dauke da fasinjoji 211 da ma'aikatan jirgin 18, ya sauka a Bangkok da karfe 3:45 na rana (0845 agogon GMT), kamfanin jirgin ya ce a cikin wani sakon Facebook.
Kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin daurin watanni 15 a gidan yari da aka yi wa Zuma bisa samunsa da laifin raina kotu a shekarar 2021, lamarin da ya haramta masa tsayawa takara a zaben da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.
"Abin da ke faruwa a Gaza ba kisan kare dangi ba ne, mun yi watsi da hakan," in ji Biden a wani taron watan al'adun Yahudawa na Amurka a fadar White House.
A badini, matsalolin rayuwa da na sana’a, sun taru sun yi wa Zango Katutu da har suka haddasa masa damuwa, bayan rabuwarsa da matan da ya aura, da kuma wasu matsaloli a cikin masana’antar.
Mawakiyar Najeriya Tems ta baiwa masoyanta mamaki ta hanyar gayyatar Wizkid da Justin Bieber, domin su hau dandamali su rera shahararriyar wakar ta mai suna Essence.
Ali Nuhu ya bayyana tarihin rayuwarsa da kuma irin gwagwarmayar da ya sha, wadda ta kai shi ga samun gagarumar nasara a masana’antar shirya fina-finai.
A wani kokari na tunawa da ‘yan mata daliban Najeriya da har kawo yanzu ba’a gan su ba, bayan sace su da mayakan Boko Haram suka yi a Chibok, an haska wani fim mai suna “Statues Also Breathe, ranar Alhamis, 4 ga watan Afrilu a birnin Legas.
Kwanan nan ne shahararren tauraro a masana’antar Adam A. Zango, ya fito yana bayanin irin matsalolin damuwa da yake fuskanta, lamarin da ya fallasa zahirin irin matsalolin da fitattun mutane a idon duniya ke fuskanta.
Domin Kari