Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFIRKA TA KUDU: An Haramtawa Shugaba Zuma Tsayawa Takara


Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma
Tsohon shugaban Afirka Ta Kudu Jacob Zuma

Kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin daurin watanni 15 a gidan yari da aka yi wa Zuma bisa samunsa da laifin raina kotu a shekarar 2021, lamarin da ya haramta masa tsayawa takara a zaben da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

A ranar Litinin, kotun kolin kasar Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin hana tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma tsayawa takarar majalisar dokokin kasar a zaben da za a yi a wannan watan, hukuncin da ka iya yin tasiri a sakamakon zaben da kuma haifar da tarzoma daga magoya bayan Zuma.

majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu
majalisar dokokin kasar Afirka ta Kudu

Kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin daurin watanni 15 a gidan yari da aka yi wa Zuma bisa samunsa da laifin raina kotu a shekarar 2021, lamarin da ya haramta masa tsayawa takara a zaben da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu, saboda kundin tsarin mulkin kasar ya haramtawa duk wanda aka yanke masa hukuncin daurin watanni 12 ko fiye da haka daga zama dan majalisa.

Former South African President Jacob Zuma, sits in the High Court in Pietermaritzburg, South Africa, Tuesday Oct. 26, 2021.
Former South African President Jacob Zuma, sits in the High Court in Pietermaritzburg, South Africa, Tuesday Oct. 26, 2021.

"An bayyana cewa an samu Mista Zuma ne da wani laifi kuma an yanke masa hukuncin daurin sama da watanni 12 a gidan yari,... don haka bai cancanci zama mamba a majalisar dokokin kasar ba, kuma bai cancanci tsayawa takara ba." "in ji hukuncin.

Zuma, wanda aka tilastawa yin murabus daga shugabancin kasar a shekarar 2018, ya samu sabani da jam'iyyar ANC mai mulkin kasar, yana kuma fafutukar kafa sabuwar jam'iyya mai suna uMkhonto we Sizwe (MK) da ya samo asali daga sunan tsohon reshen jam'iyyar ANC.

Supporters sing and chant at the Mehlareng stadium in Tembisa during a recruitment drive for the newly launched Umkhonto We Sizwe political party backed by former South African President, Jacob Zuma on January 21, 2024. (Photo by EMMANUEL CROSET / AFP)
Supporters sing and chant at the Mehlareng stadium in Tembisa during a recruitment drive for the newly launched Umkhonto We Sizwe political party backed by former South African President, Jacob Zuma on January 21, 2024. (Photo by EMMANUEL CROSET / AFP)

Sakatare-janar na MK Sihle Ngubane ya shaidawa manema labarai na cikin gida cewa hukuncin na ranar Litinin bai shafi yakin neman zabensa ba. Ya kara da cewa, shugabannin jam’iyyar za su gana, su kuma dauki kwakkwaran mataki daga Zuma.

A shekarar 2021 daurin da aka yi wa Zuma ya haddasa tarzoma a KwaZulu-Natal inda mutane sama da 300 suka mutu, lamarin da ya rikide zuwa wawushe-wawushe.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG