Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Na Karban Haraji A Jihar Neja


'Yan bindiga da ke kai hare-hare.
'Yan bindiga da ke kai hare-hare.

Yayin da ake ci gaba da samun tabarbarewar tsaro, gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da karbar harajin da ‘yan bindiga ke yi a jihar kamar yadda wasu majiyoyin suka rawaito.

Kwamishinan kananan hukumomin jihar, harkokin masarautu da tsaron cikin gida, Mista Emmanuel Umar, ya tabbatar da hakan a Minna, inda ya ce a yanzu ‘yan bindigar na karbar harajin daga manoman jihar domin ba su damar girba amfanin gonakinsu.

Ya ce gwamnatin jihar ta umarci al’umma da su yi watsi da wannan umarni domin ta samar da matakan tsaro musamman don kare manoma.

“Wasu mahara a Rumbun Giwa da ke karamar hukumar Mashegu ta Jihar Neja kwanan nan sun rubuto a karkashin wani suna Kungiyan Manuma, inda suka umurci duk manoma da su biya wasu takamaimai haraji kafin su samu damar noma su girbe amfanin gonakinsu.

“Muna sane da cewa Allah ya albarkaci manomanmu da yawa a wannan lokacin noma kuma gwamnati ta kudiri aniyar tallafa musu.

Wadannan miyagun mutanen suna kokarin kwace wa manoman ne; kamata ya yi al’umma su tallafa wa jami’an tsaro. Muna iya kokari don ganin cewa maharan ba su da sarari a cikin al'ummominmu," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga al’umma da su jajirce domin dakile ayyukan ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ta hanyar baiwa jami’an tsaro bayanai masu amfani domin daukar matakan da suka dace.

Ya ce gwamnatin jihar ta kammala shirye-shiryen daidaita ayyukan ‘yan banga a fadin jihar domin tallafawa jami’an tsaro.

XS
SM
MD
LG