rahotannin dake fitowa daga birnin Legas na nuna cewa mutane da dama basu fito ba domin zabe, duk da yake an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a birnin.
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa tare da hadin gwiwar hukumar tallafawa yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta dawo da wasu yan Najeriya 326 daga kasar Libya ta babban filin jiragen sama na Murtala Muhammed dake Legas.
A yayinda ya rage kasa da sao'i 48 a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, shugabannin al’umma a yankin kudancin Najeriya na ci gaba da kira ga 'yan kasa musanmman matasa dasu fito domin kada kuri’unsu domin samun nasarar zaben.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya maida martini ga ofishin yakin sake neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, game da zargin da jami’in yada labarai Festus Kiyamo ya yi cewa jakadan Amurka na goyon bayan jam’iyyar adawa ta PDP da kuma Atiku Abubakar.
Yanzu haka dai ana zaman dar dar a fadar gwamnatin jihar Legas sakamakon matakin da Majalisar Dokokin Jihar suka fara dauka na neman tsige gwamnan Jihar Akinwumi Ambode, bisa laifin kasa gabatar da kasafin kudin bana.
Shan miyagun kwayoyi da jabun magunguna su na cikin matsalolin da ke damun gwamnati, abin da yanzu haka wata kungiya mai zaman kanta ta dauki alkawarin taimaka gwamnati domin magance wannan matsalar.
Rundunar hukumar Kwastam ta daya mai kula da jihohin Legas da Ogun ta kama wasu kayayyaki da aka hana shigo da su cikin kasar, wanda ya sa kasar ta kara samun kudaden shiga sosai.
Kwamitin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa don karin albashin ma'aikata, ya fara aiki gadan gadan.
Hankali ya sake komawa kan irin namijin kokarin da matan karkara ke bayarwa musamman ma a fannin noma da tattalin arziki da zamantakewa.
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana goyon bayansa ga tsohon mataimakinsa dan takarar shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar.
Masu sana'oin hannu na ci gaba da samun riba a lokutan zabe musaman masu sana'ar buga hotuna ko kuma "fosta" na 'yan siyasa.
A karon farko an shirya gudanar da taron Kungiyar Tashoshin Jiragen Ruwa Na Duniya a Najeriya, taron wanda a karon farko Ake gudanar Dashi a wata nahiya daba ta Turai zai duba hanyoyin bunkasa sufurin Jiragen ruwa tare da kasuwanci da tsaron tekunan duniya.
EFCC ta gurfanar da wani dan Najeriya gaban kotu, bisa zargin yin amfani da sunan shugaban ma’aikatar Shari’ar Amurka, wajen danfarar mutane ta kafofin sadarwa.
Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ya kulla wata yarjejeniya da wasu Bankuna na kasashen waje, da zata taimaka wajen inganta harkokin Man fetur da iskar Gas da kasar ke da su.
Hukumar NAFDAC mai kula da inganci abinci da magunguna ta Najeriya ta kama kwalaben magungunan tari kimanin miliyan biyu da rabi, bayan da gwamnati ta haramta sayar da duk magungunan tari dake dauke da sinadarin Codeine.
Kasa da sa'o'i 24 da ganawar da Shugaba Buhari yayi da takwaransa na Benin Patrice Talon inda suka duba batun magance matsalar fasa kwori musamman na shinkafa da ake yi tsakanin kasashen biyu.
A yayinda jam’iyar PDP ke ci gaba da murna da kuma shagali bisa sauya sheka da wasu yan majalisar dattijai da wakilai sukayi daga jami'iyar APC mai mulki, rashin komawan yayan jam’iyar APC daga yankin kudu maso yammacin Najeriya zuwa PDP ya kara nuna alamun cewar jam’iyar PDP bata da karbuwa a yankin kudu maso yanmacin najeriya
Domin Kari