Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ware duk ranar 18 ga watan Yuli a matsayin ranar tunawa da Nelson Mandela, shugaban Afirka ta Kudu kuma wanda yayi rajin neman ‘yancin bakaken fata.
An kamala wani taron kasa da kasa domin inganta adabin baka na yankin nahiyar afrika, taron da kungiyar raya adabin baka ta duniya ta dauki nauyin gudanar dashi a birnin Lagos.
Kokarin da kungiyar raya kasashen ketare da gwamnatin Amurka ke yi na tallafawa Najeriya ta zama mai dogaro da kai ta fuskar abinci, hukumar USAID ta shirya taron bita ga wasu malaman bangaren noma na jami’oin Najeriya domin samun nasarar shirin.
A yau Laraba ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ke kammala ziyarar daya kai Najeriya domin habaka huldar tattalin arziki da Al’adu tsakanin Kasashen biyu.
‘Yan Najeriya naci gaba da tofa albarkacin bakunan su game da cancanta ko rashin cancantar mataki na gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka na karrama Cif MKO Abiola da ake ikirarin ya lashe zaben shekara ta dubu da dari tara da casa'in da uku
Matsalar tattalin arziki a Najeriya ya ragewa kasuwar China Town dake birnin Legas armashi.
Gwamnatin Najeriya ta fara aiki da sabon haraji da ta saka wa kamfanonin tabar sigari da na barasa abin da kuma ke samun martani daga jama'ar kasar.
Wasu gungun likitoci a Najeriya sun kirkiro wata mahajar da za ta rage cinkoso ko tsawon lokutan ganin likita a Najeriya.
Wata kungiyar al’ummar ‘yan arewacin Najeriya dake zaune a kudancin kasar ta gudanar da taron zaman lafiya tare da nuna rashin jin dadi game da tabarbarewar tsaro a kasa baki daya.
Tsakanin Najeriya da sauran kasashen duniya ana asarar biliyoyin dalar Amurka, sakamakon ayyukan ‘yan damfara da aka fi sani da ‘yan 419, ko Yahoo-yahoo Boys.
A yayin da gwamnatin Jihar Legas ke barzanar rufe mayankar da ke Agege, mahauta da dillalan shanu sun yi barazanar daina kai shanu Jihar, lamarin da ka iya haifar da karancin nama.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 25 ga watan Afrilu na kowacce shekara domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da ake kira Malaria.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wasu tarin makamai da alburusai kimanin 400 a cikin watanni shida, a wani yunkuri na raba al’umma da makamai gabanin zaben 2019.
An kammala wani babban taron habaka harkokin kasuwanci da kudi na musulunci da aka gudanar tare da hadin gwiwar ma’aikatar kudi ta Najeriya, wanda kungiyar habaka masana’antu masu zaman kansu a nahiyar Afirka ta shirya a Legas.
A ci gaba da rangin da yake yi a wasu kasashen nahiyar Afirka sakataren harkokin wajen Amurka zai isa Najeriya yau litinin, inda a gobe talata zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari don tattauna yaki da ta'addanci da harkokin tattalin arziki.
Bayode Olawumi na jihar Lagos ya zama sarkin karatun duniya bayan da ya kwashe kwanaki biyar ko sa'o'i 120 ya na karatu ba tsayawa, har ya karance littafai 17, lamarin da ya sa ya doke Diparo Sharmak na kasar Nepal wanda ya yi sa'o'i 113 da mintuna 15 yana karatu
Kasa da mako guda bayan da kungiyar Transparency International ta ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na komawa baya, wata sabuwar kungiyar matasa mai suna New Nigerian Nationalist, ta fito tana tattaki daga Lagos zuwa Abuja domin jawo hankalin kasar a tashi tsaye a yaki cin hanci da rashawa kafin su ruguza kasar
Akasarin 'yan arewacin Najeriya dake zaune a Legas, sun ce kafa rundunonin 'yan sanda na jihohi, tamkar ayyana raba Najeriya ne a saboda su kadai suka san ukubar da suke sha a yanzu haka ma a kudu
Ana samun shinkafa cikin sauki a Legas bayan yarjejeniyar da jihar ta kulla da jihar Kebbi inda ake noman shinkafar sannan kuma a kawo Legas domin sarrafawa a sayarwa jama'a.
Domin Kari