Wani rahoto da ofishin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ya nuna cewa Najeriya na daga cikin kasashen duniya da cinikayya tsakanin kasar da Amurka ke ci gaba da habaka.
Rahoton ya nuna cewa kamfanonin Amurka da ke siyar da kayayyaki da kudinsu ya kai na fiye da dala biliyan biyu a shekarar da ta gabata wanda ya kara da kaso 60 cikin 100 idan aka kwatanta da shekara ta 2015 da kuma 2016 a yayin da Najeriya ta sai kayayyaki da ya kai na dalar Amurka biliyan 7.
Akasarin kayayyakin da ake cinikayya tsakanin Najeriya da Amurka dai ya ta'allaka ne akan ma'adanan man fetur da motoci da sauran kayayyaki na masana'antu. Dr. Dauda Muhammad Kontogora wani masanin tattalin arziki da saka jari ya ce bayannan yadda ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya tattara kan matsalolin zuba jari a Najeriya sunayi ne somin su watsa shi ga 'yan kasuwar da ke so su zuba jari a kasashen da bayanin ya shafa, Rahoton yayi magana akan cin hanci da rasahawa da kuma ta'addanci.
Saurari Rahoton da wakilinmu Babangida Jibrin ya aiko daga Lagos
Facebook Forum