Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magoya Baya Na Tsokaci Game Da Sauya Shekan Yan Jam'iyar APC


A yayinda jam’iyar PDP ke ci gaba da murna da kuma shagali bisa sauya sheka da wasu yan majalisar dattijai da wakilai sukayi daga jami'iyar APC mai mulki, rashin komawan yayan jam’iyar APC daga yankin kudu maso yammacin Najeriya zuwa PDP ya kara nuna alamun cewar jam’iyar PDP bata da karbuwa a yankin kudu maso yanmacin najeriya

Rashin komawar yayan jam’iyar APC daga yankin kudu maso yammacin Najeriya zuwa PDP ya kara nuna alamun cewar jam’iyar PDP bata da karbuwa a yankin kudu maso yanmacin najeriya, yankin da kabilar yarbawa sukafi yawa, wayanda kuma ake ganin suna goyon bayan jam’iyar APC sama da kasa.

Daga cikin yan jam’iyar APC da suka sauya sheka akasarin su sun koma jam’iyar ADC ne, wata sabuwar jam’iya mai alaka da tsohon shugaban kasa Dr Olusegun Obasanjo, wanda kuma ya kudiri aniyar ganin kawo karshen mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shekara mai zuwa na 2019.

Daya daga cikin yan majalisar daga jihar Oyo sanata Adesoji Akanbi da a jiya aka ce ya koma ADC ya musanta wannan labarai, inda yace shi yana nan daram dakam cikin APC.

Wasu mutane da dama na cewa dalilin da ya sa yan jam'iyar APC ke sauya jam'iya zuwa PDP , saboda basa son gyara ne, yayinda wasu da dama ke dora laifin akan gwamnatin Muhammadu Buhari wanda haka ka iya janyo ci baya ga jam'iyyar APC mai mulki.

Wannan lamarin ya sanya mutane nazarin cewa ko yan majalisun da suka sauya sheka zasu iya cin zabe ba tare da Buhari ya daga hannun su ba, shine abin a jira a gani.

saurari rahoton Babangida Jibril

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:31 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG