Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Kasuwar Masu Sana'ar Buga Hotunan 'Yan Siyasa Ta Bude


Masu sana'oin hannu na ci gaba da samun riba a lokutan zabe musaman masu sana'ar buga hotuna ko kuma "fosta" na 'yan siyasa.

Yanzu dai ko ina ka waiwaya tsakanin birane da karkara, duk inda ka duba hotunan 'yan siyasa ne da suka fito neman takara ke manne gabanin zaben 2019.
Manyan tituna na cike makil da fostocin 'yan siyasa a ko wanne lungu da sako, duk da cewa wasu gwamnatoci sun hana lika fosta amma duk da haka, ba su guji yin hakan ba.
Ko da yake, jama'a da dama na cewa dokar ba ta da wani tasiri, saboda masu bincike na cewa magoya bayan masu dokar ne ke kan gaba wajen lika hotunan 'yan takarar su.
Dalilin kafa dokar hana lika fosta shi ne hana gurbata muhalli da Kuma tsaftace birane da kauyuka, wasu daga cikin masu buga fostocin da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka ya tuntube su, sun ki cewa uffan game da aikin na su.
Sai dai wani da bai yarda a ambaci sunansa, ya ce suna samun irin wannan ayyukan sosai a ko da yaushe.

Wani mai sharhi a bangaren yadda al'umma ke kallon wannan lamari, Shu'aibu Yusuf, ya ce ya kamata duk wanda ya fito neman takara ya yi amfani da hanyoyi na daban da ake da su kamar talbijin ko rediyo da dai sauran kafoffin sadarwar zamani irin su Facebook, Twitter, da Instagram domin aika sakkoninsu.

Al'umma dai na fatan 'yan siyasar Najeriya za su yi koyi da takwarorinsu na kasashen duniya wajen gudnar da zabe mai tsafta.

Lika Postocin Yan Siyasa Ya Sabawa Doka 2'34
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG