Gwamnatin Jihar Legas ta rattaba hannu da wasu 'yan kasuwa da za su taimaka ma ta wajen rarraba ko sayar da shinkafar da ta sarrafa mai suna Lake View rice ta yadda jama'ar garin za su iya siya.
Jihar Legas ta fara sayar da shinkafar ne a bara bayan yarjejeniyar da ta kulla da Jihar Kebbi inda ake noman shinkafar sai kuma a kawo Legas domin sarrafawa sannan a fitar a sayar.
Wannan rattaba hannun da manyan 'yan kasuwa da Gwamna Akinwunmi Ambode yayi zai taimaka wajen samar da isasshen shinkafa a ko'ina a jihar yayin lokacin kirsimeti da sabuwar shekarar da za a shiga cikin sauki.
Wasu mazauna jihar sun nuna gamsuwarsu da wannan mataki inda wata ta shaida cewa,
"Na zo tun da safe domin neman shinkafar Lake Rice kuma na yi sa'ar samunta cikin sauki."
Wata kuma tace ta ji labarin shinkafar daga wurin kawayenta amma kan farashi dabam dabam suka bayyana sun siya, " Wata tace min dubu 8, wata kuma tace dubu 10, wata kuma 12," inji ta.
Shi dai wannan shinkafar mai nauyin kilo 50 ake sayarwa akan naira dubu 12, sai kuma mai nauyin kilo 25 kan naira dubu 6 sannan kuma rabinsa mai nauyin kilo 10 a kan naira 2500.
Yarjejeniyar da Jihar Kebbi ta kulla da jihar Legas na samar shinkafa, an yi ta ne domin taimaka wajen samar da ayyukan yi ga jama'ar jihohin biyu da kuma kawo karshen shigowa da shinkafa daga kasashen waje. Kamar yadda gwamna Atiku Bagudu ya bayyana cewa,
" Yawan mutanen da ke cikin Najeriya ya fi miliyan 300. To ko sayar musu da abinci wata hanyar arziki ce wadda ta nan kawai za a iya samun kudi daga shinkafa fiye da yadda muke samu daga mai ballanta ma shinkafa abu ne da ake siya ko'ina a duniya."
Ga rohoton Babangida Jibril don karin bayani.
Facebook Forum