Alkaluma daga kungiyar sufurin sama ta kasa da kasa IATA a takaice sun nuna cewar Afrika ce ta ke samun bunkasa a fannin sufurin jiragen sama cikin gaggawa a shekaru ishirin masu zuwa kasancewar bukatar sufurin jiragen saman zai ninka.
A jiya Asabar ne al’ummar kasar Mauritania suka kada kuri’a a zaben farko da aka yi a kasar ba tare da wani shugaban kasa mai ci tun bayan juyin mulkin shekarar 2008.
A wani mataki mai al’ajabi, shugaban Amurka Donald Trump yace ya dakatar da batun aikin korar dubban bakin hauren da basu da takardun zaman Amurka da jami’an hukumar shige da fice zasu fara a yau Lahadi, har sai ‘yan makwanni masu zuwa.
Shugaban ‘yan adawa a kasar Venezuela Juan Guaido a jiya Juma’a yace ya fada a yayin wata ganawa da shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet muhimmancin kawar da shugaba Nicholas Maduro domin kawo karshen wahalar da mutane ke sha.
Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta nemi ta sasanta tsakanin gwamnatin sojin Sudan da ‘yan adawa, a matsayin ramawa Sudan rawar gani da ta taka a lokacin tattaunawar zaman lafiyar Sudan ta Kudu a bara.
Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar da wasu sababbin hotuna wadanda ta ce sun dada tabbatar da cewa kasar Iran ce ta kai wa tankokin mai hari a tekun Oman a makon da ya gabata.
A jiya litinin ne, Tsohon shugaban kasar Masar Mohammaed Morsi, wanda shi ne shugaban kasar na farko da aka zaba bisa tsarin dimokradiyya aka kuma tsige shi, ya yanke jiki ya fadi kasa ya mutu a yayin wani zaman kotu.
Hadaddiyar kungiyar dillalan shanu da kayan abinci, ta ce za ta dakatar da duk wata harkar fataucin abinci a duk fadin kasar i dan har gwamnati ba ta dauki matakin rage yawan harajin da ake karba daga mambobinta a wasu hanyoyin kasar ba.
Jami’an tsaron farin kaya na "sibil difens" a jihar Adamawa sun samu nasarar murkushe masu satar mutane domin neman kudin fansa. Wannan nasarar ta na zuwa ne a lokacin da jama’a ke kasa barci sakamakon ayyukan masu garkuwa da jama’ar.
An kashe akalla mutane goma kana wasu 23 kuma sun jikata a wani bam da ya tashi a cikin mota a jiya Asabar a wata babbar hanyar da jama’a ke harkoki a birnin Mogadishu, a cewar shedun gani da ido da ma’aikatan kiwon lafiya.
Yarima mai jiran gado a Saudi Arabia ya zargi kasar Iran da kai hare hare a kan jiragen dakon mai a kan tekun Oman kana ya yi kira ga kasashen duniya su dau kwakkwarar mataki a kan wannan batu.
Jami’ai a Saudi Arabia sun ce basu amince da bude gidan rawa da aka ce an bude da yammacin ranar Alhamis a Jeddah, birni mafi girma na biyu a Saudiya.
Sakataren tsaron Amurka Pat Shanahan yace Amurka tana kokarin kulla wani babban hadin kan kasa da kasa a kan batun Gabas ta Tsakiya game da harin da aka kaiwa jirgen dakon mai a kan tekun Oman.
An kashe akalla mutane 95 a tsakiyar Mali a jiya litinin a lokacin da 'yan bindiga suka kaiwa wani kauye hari a cikin dare, inda suka bude wuta a kan jama’a kana suka cinnawa gidajen mutane wuta.
A jiya Litinin ne 'yan jam’iyar Demorats a majalisar walikan Amurka suka cimma yarjejiya da Ma’aikatar Shari’ar Amurka cewa zata gabaratwa majalisa muhimman takardun da mai bincike na mussaman Robert Mueller ya tattara yayin da yake gudanar da binciken.
An kama daruruwan magoya bayan shguaban ‘yan adawa Kamaru, Maurice Kamto, wanda ke fuskantar zargin cin amanar ‘kasa bayan da ya jagoranci zanga-zanga da yin imanin shine ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Oktoba.
Hukumomi a Ghana sun bayyana fargabar samun hare haren ‘yan ta’adda a cikin wannan lokaci, lamarin da yasa hukumomin tsaron kasar suka fara daukar matakan sa ido a kan harkokin jama’a tare da yin gargadi ga jama’a su kula kuma su taimakawa jami’ai da bayanai.
A yau Talata goma sha daya ga watan Yunin shekarar dubu biyu da ashirin ne majalisar dokokin Najeriya ta ciko tara zata fara aiki, baya an zabi shuganannin majalisar.
Shugabannin masu zanga zanga a Sudan suna kira ga mutanen kasar su kara kaimi a ayyukan kalubalantar gwamnatin sojan kasar, biyo bayan amfani da karfin tuwo da sojojin suka yi a kan mutane a lokacin wani zaman dirshe.
Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya aikawa takwarar aikinsa na India Narendra Modi da wasikar dake kira ga shirya zaman sasantawa tsakanin su.
Domin Kari