Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Amurka Tace Dole A Kawo Mata Muhimman Takardun Binciken Trump


Donald Trump
Donald Trump

A jiya Litinin ne 'yan jam’iyar Demorats a majalisar walikan Amurka suka cimma yarjejiya da Ma’aikatar Shari’ar Amurka cewa zata gabaratwa majalisa muhimman takardun da mai bincike na mussaman Robert Mueller ya tattara yayin da yake gudanar da binciken.

Muller ya kwashe kimanin shekaru biyu ya gudanar da bincike a kan ko shugaban kasa Donald Trump ya yi katsalandan a binciken da ake yi a kansa, na shishigin kasar Rasha a zaben Amurka na shekarar 2016.

Dan majalisa Jerrold Nadler, shugaban komitin shari’a a majalisa wakilai, yace ma’aikatar shari’a zata bude musu muhimman takardun binciken Muller kana ta gabatar musu da muhimman shaida domin su tantance ko Trump ko kuma wani ya yiwa binciken shisshigi ko aikata ba daidai ba

Nadler ya kara da cewa dukkani mambobin komitin da suke zaman sauraren bahasin na Democrats da Republican zasu samu damar ganin takardun kuma zai basu damar aiwatar da alhakin da kundin tsarin mulki ya dora musu kana su yanke shawara a kan zargi da Muller ya yiwa shugaban kasa.

Nadler yace bisa wannan yarjejeniya ce, zai janye kada kuri’ar da aka shirya yi a yau Talata a kan yiwuwar aza lafin rashin mutunta majalisa a kan Atoni Janar Billiam Barr saboda kin bayyana gaban majalisar ya bata bayanan da take bukata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG