Shugaban hadaddiyar kumgiyar, Dakta Muhammad Tahir ya shaida wa Muryar Amurka cewa, tun bayan wata ziyarar da su ka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa har iyau bai ce musu uffan ba. Ya ce sun yi wa shugaban kasar uziri saboda abubuwa sun yi masa yawa, amma su na tuna masa ziyarar da su ka kai masa a kan yawan haraji da ake karba a kan hanya.
Shugaban reshen kungiyar masu fataucin shanu a jihar Akwa Ibom, Alhaji Muhammad Mijinyawa shi ma ya dora muryarsa inda ya koka a kan yanda ake kwace wa mutanensu kudade a kan hanya da sunan haraji alhalin babu wadannan haraji a doka.
Mista Alex Avakaa, shugaban kungiyar a jihar Binuwe ya ce, jihar Binuwe na daya daga cikin jihohin da aka fi samun matsalar yawan haraji. An siyasantar da batun a jihar Binuwe sosai, saboda bisa binciken da muka gudanar, mun tarar cewa a jihar kadai akwai shingayen karbar haraji 360 da aka kafa ba bisa ka'ida ba a hanyoyin tarayya da na jiha da kuma na karkara.
Anan, zaka ga wani na ikirarin cewa wani babban jami'in gwamnati ne ya sa shi karbar harajin. Hakan kuma na gurgunta tattalin arzikin jihar da na kasa baki daya. Mu na kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin magance wannan batu.
A kan wannan batun ne Malam Abdullahi Yuguda, wani mamban kungiyar, na ganin gina hanyar jirgin kasa zai taimaka ainun wajen saukaka matsalar yawan haraji a hanyoyin Taraba, Binuwe, da kuma Kuros Riba.
Wakilin mu Alphonsus Okoroigwe nada karin bayani:
Facebook Forum