Shirye-shirye sun kammala don kaddamar da majalisar dokokin Najeriya ta tara a Talatar nan da zai kasance da bayyanar sabin shugabannin majalisar.
Jam'iyyar APC mai rinjaye ta kara dagewa don 'yan takarar da ta tsayar da suka hada da Sanata Ahmed Lawan a majalisar dattawa da Femi Gbajabiamiala a majalisar wakilai su samu nasara.
Tsohuwar majalisa ta takwas ta kammala aiki a makon jiya inda tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya ba wa kowa dama ya yi takarar yadda ya ke ganin majalisar ta gudanar da aiki a tsawon shekaru hudu.
Sabbin shugabannin majalisar za su nuna ko gwamnatin shugaba Buhari za ta gamsu da hulda da majalisar ko kuwa a'a.
Tsohon shugaban kwamitin labaru na majalisar wakilai ta takwas, Abdulrazak Namdas, na daga wadanda su ka janye daga takarar kakakin majalisar wakilai don marawa muradun jam'iyyar APC yana mai cewa hakan ba zai maida su 'yan amshin shatar sashen zartarwa ba.
Ga hirar Abdulrazak Namdas da Nasiru Adamu El Hikaya a kan batun majalisar:
Facebook Forum