Bakin haure sama da 80 da ke cikin jirgin ruwan nan na kasar Spain da ya cecesu a kan teku, sun taka doron kasa a karon farko, bayan da suka kwashe kwanaki 20 a cikin jirgin da ya yi ta galantoyi akan teku.
Shugaban Amurka Donald Trump, ya fada wa shugaban kungiyar ma'abuta bindiga ta NRA cewa, batun gudanar da kwakkwaran bincike kan duk wani da zai sayi bindiga, ba ya cikin matakan da za a dauka wajen magance matsalar harbe-harbe a Amurka.
Biyo bayan sake cafke jagoran gungun masu satar mutanen nan na jihar Taraba a Unguwar Hotoro da ke birnin Kano, bayan da tun da farko sojoji suka bude wa ‘yan sandan IRT wuta a jihar Taraba suka hallaka jami’an ‘yan sandan uku da suka kamo dan ta'addan suka kuma sake shi ya kama gabansa.
Hukumomi a kasar Ghana sun kara kaimi a yaki da cutar cizon sauro ko Maleriya, inda shirin yaki da cutar ke cigaba da samun tallafi da kuma kwarin gwiwar aiwatar da tsare tsare domin ganin an rage illar da cutar ke yiwa al’umma musamman kananan yara da mata masu juna biyu.
Mataimakin gwamnan jahar Nasarawa, Dakta Emmanuel Akabe ya tsallake rijiya da baya, bayan da wasu da ake kyautata zaton mafasa ne su ka tsare matafiya a hanyar Lafia zuwa Akwanga, lamarin da ya yi sanadin rasa rayukan ‘yan sanda shida.
Wasu bakin hauren da su ka zaku, sun yi ta tsalle daga wani jirgin ruwan Spain da ya ceto su, su na fadawa cikin tekun Bahar Rum jiya Lahadi a yayin da jirgin ruwan Spain din mai suna Open Arms ke kokarin neman tasha marar hadari da zai tsaya.
Yawan hare-hare da sace mutane a jahar Kaduna ya tsananta cecekuce tsanin shugabannin addinai ta yadda harma majalisar limamai da malamai ta jahar Kaduna ke Allah wadarai da al'amarin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta bada sanarwar kama wasu mutane biyar sakamakon rikicin da ya auku a wata kasuwa da ke jihar, haka kuma mutane hudu sun samu raunuka a wannan fada tsakanin Hausawa da Yarbawa.
Kimanin dalibai 50 ne da suka yi nazari a fannonin kiwon lafiya daban daban a jami’o’in kasashen waje ke samun horon kwarewa dana sanin makamar aiki a asibitin koyarwa na Aminu Kano a Najeriya.
Shugaban Koriya Ta Kudu, Moon Jae-in, ya ce kasarsa za ta yi farin cikin hada hannu da Japan don warware takaddar cinakayyar da ke dada tsanani tsakaninsu, muddun Japan ta yadda su hau teburin shawara.
Kasar Isira’ila ta haramta shiga ma wasu ‘yan majalisar dokokin tarayyar Amurka biyu jiya Alhamis, wanda wannan zai tayar da wata sabuwar takaddama a muhawarar da ake yi, game da irin goyon bayan da Amurka ke bai wa wannan muhimmiyar kawar ta a yankin Gabas Ta Tsakiya.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa shugaban 'yan Shia na IMN Ibrahim Elzazzaky ya so zullewa ne ta amfani da damar da kotu ta ba shi ta neman magani a Indiya.
Manyan manoma da ‘yan kasuwa a Najeriya sun fara mayar da martani game da kokarin inganta cinikin kayan abincin da aka noma a cikin gida, da ya sa shugaba Buhari ya ba shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele umurni da ya daina bawa masu shigowa da kayan abinci daga kasashen waje tallafi.
Rubu’i biyu na magungunan cutar Ebola da aka gwada a Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo, sun yi matukar inganci ta yadda ma za a fara bai wa masu fama da cutar ta Ebola.
Gwamnatin Trump ta yi shelar bullo da wani tsari jiya Litini, wanda zai hana bakin hauren da ke cikin kasar samun takardar zama dindindin ko ta zama dan kasa, muddun sun dogara ne ga taimakon gwamnati, irin na kiwon lafiya, da abinci ko kuma muhalli.
Yayin da ana ci gaba da gudanar da bukukuwan babbar Sallah, shuagabannin al'ummar Musulmi a jihar Imo sun yi kira ga jama'ar Najeriya da su kasance masu neman zaman lafiya a ko yaushe, don kawo karshen kalubalolin rashin tsaron da kasar ke ta fama da su.
Hukumar kula da lamuran ruwan sama da na koguna NIHSA ta anakaradda jihohin Najeriya 15 cewa za a samu ambaliyar ruwa a cikin su da hakan tuni ma har ya haddasa asarar rayuka.
Yayin da dokar hana kai-komo, irin wadda yankin Kashmir bai taba gani, ke ci gaba da aiki, Firaministan Indiya Narendra Modi ya yi wa ‘yan yankin na Kashmir alkawarin fara shiga, abin da ya kira, “sabuwar makoma.
Jiya Alhamis, magadan gari sama da 200 a Amurka, sun bukaci ‘yan majalisar dattawa da su dawo daga hutun lokacin barazar "Summer", su rattaba hannu kan kudurin dokar dakile wanzuwar bindigogi.
A ranar Laraba da safe ne aka yi ta tada jijiyar wuya a zauren majalisar dokokin kasar Kenya bayan da wata ‘yar majalisa Zuleika Hassan ta shiga zauren majalisar da jinjirin wata biyar.
Domin Kari