Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

India Na Ci Gaba Da Sauya Matsayin Kashmir Na Mai Cin Gashin Kai


Kashmir
Kashmir

Yayin da dokar hana kai-komo, irin wadda yankin Kashmir bai taba gani, ke ci gaba da aiki, Firaministan Indiya Narendra Modi ya yi wa ‘yan yankin na Kashmir alkawarin fara shiga, abin da ya kira, “sabuwar makoma.

Wannan alkawarin ya biyo bayan shawarar da gwamnatinsa ta yanke ta soke ‘yancin cin gashin kai na musamman da aka bai wa yankin, da kuma maido da yankin karkashin ikon Indiya kai tsaye.

A wani jawabin da aka yada ta gidan talabijin da rediyo jiya Alhamis, Modi ya kare matakin soke tanajin kundin tsarin mulkin nan wanda ya tanaji bai wa yankin na Kashmir ikon kafa dokar kansa, da cewa wannan tanajin ya janyo ma yankin cibaya, wanda hakan ya haifar da ayyukan ta’addanci, kuma Pakistan mai jayayya da Indiya na amfani da yankin a matsayin wani makami ta wajen ingiza wasu mutanen yankin.” Yanzu kasar Indiya za ta ceto yankin daga ta’addanci da ‘yan ta’adda, a cewarsa.

Indiya ta dora ma Pakistan laifin ingiza tashe-tashen hankulan, da ‘yan aware su ka kwashe shekaru gommai suna haddasawa a yankin na Himalaya da kasashen biyu, kowacce ke ikirarin na ta ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG