Malam Bashar Uwakwe shine shugaban majalisar Musulmi na jihar Imo, kuma ya ce "Sakona ga 'yan Najeriya shine su nemi zaman lafiya, su kuma kaurace wa hargitsi da kuma duk abin da na iya tada hankalin jama'a.
Ya kuma kara da yin kira ga kasar, daga hukumomi zuwa talakawa, da kowa ya tabbatar da zaman lafiya a duk inda yake, saboda wuce gona da iri baida wani amfani.
Sai kuma Oba Musibau Oladeji, sarkin Yarbawa na jihar Imo ya dora akan batun cewa "Mu rungumi zaman lafiya saboda rashin tsaro na yiwa kasar barazana a halin yanzu. Yace yakamata gwamnati ta tashi tsaye ta dauki kwakkwarar mataki akan wannan batun, saboda matukar ba a mayar da hankali akan wannan ba, hakan na iya wargaza kasar.
Daga bisani, mai taimakawa gwamna Emeka Ihedioha na jihar Imo akan lamuran Arewa, Hon. Hassan Yahaya Babidi ya yi matukar yabawa gwamnan don goron Sallar da ya raba wa al'ummar Musulmi a wannan lokacin Sallah.
Shima Garkuwan Hausawa na jihar Imo, Alhaji Suleiman Ibrahim Suleiman ya mika sakon godiya ga gwamnan.
Ga rahoton wakilin Sashen Hausa Alphonsus Okoroigwe daga Owere:
Facebook Forum