Fadan da ya kaure tsakain matasan Yarabawa da Hausawa da ya yi dalilin jikata mutane da dama, ya so ya rikide ya zama fadan kabilanci, wanda a cewar masana lamarin ka iya yin muni idan ba a dauki mataki da wuri ba.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta Legas, ta hannun kakakinta, DSP Bala Elkana, ta ce mutane hudun da aka kama ana gudanar da bincike a kansu, kuma da zarar an kammala binciken za'a gurfanar da su a kotu.
DSP Bala ya ce an fara fadan ne tsakanin mutum biyu a wata kasuwar da ke Okeruwa ta shiyar Alumosho, lamarin da ya rincabe bayan mutane biyun sun samu goyon baya daga ‘yan kabilansu.
Sai dai bangaren Hausawa ya ce akasarin wadanda aka kaman Hausawa ne, a yayin da aka kyale 'yan bangaren abokan fadansu, zargin da rundunar ‘yan sanda ta ce tana bincike a kai.
Babangida Jibrin ya aiko mana da rahoto daga Legas:
Facebook Forum