Wannan kira na zuwa ne bayan harbe-harben kai mai uwa da wabin nan biyu da aka yi a karshen mako, da su ka yi sanadin mutuwar mutane 31 a jihohin Texas da Ohio.
Babbar haduwar magadan garin Amurka, wadda ke wakiltar birane 214, wadda kuma shugabanninta su ka hada da ‘yan Republican da ‘yan Dimokarat, ta gaya ma Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar dattawa dan Republican Mitch McConnell da kuma jagoran marasa rinjaye dan Dimokarat Chuck Schumer, cewa da matukar bukatar Majalisar Dattawa ta amince da kudurin, wanda tuni Majalisar Wakilai ta kada kuri’ar amincewa da shi a watan Fabrairu.
Kudurin dokar ya tanaji binciken yanayin duk wani mai son sayen bindige, ya kuma tanaji tsawaita lokacin dakon amincewa da saye daga kwanaki uku, kamar yadda yake a yanzu, zuwa kwanaki 10 musamman ma idan binciken farko ya kai ga janyo ayar tambayoyi game da yanayin mai niyyar sayen bindigar.
Schumer ya yi kiran da Majalisar Dattawa ta amince da kudurin, to amma McConnell ya ki a kada kuri’ar saboda baya goyon bayan kudurin dokar.
Facebook Forum