Jami'i mai kula da al'amuran mu'amala da jamma'a Muntari Yusuf Ibrahim ne ya fitar da sanarwa cewa “an lura da yadda ake samun gajimare a wasu yankunan arewacin kasar kamar Borno, Taraba, Gombe, Bauchi da Kano, wanda ake sa ran zai kada yammaci ya haifar da yanayi makamancin na farko a wasu birane."