Shugaban mayakan hayan Rasha na Wagner Yegeny Prigozhin, ya yi alkawarin bayyana wa gwamnatin Ukraine mabuyar dakarun Rasha kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a bisa wani rahoton Washington Post na jiya Lahadi, wanda ya ambato takardun bayanan sirrin Amurka.
Mayakan Wagner sun kasance a kan gaba a barin wutar da Russia ta ke yi domin karbe ikon birnin Bakhmut. A watan ne Prigozhin ya yi tayin bayyana wa jami’an sirrin Ukraine inda dakarun Rasha suke a madadin sojojin na Ukraine su janye daga yankin, jaridar the post ta ruwaito. Takardar ta ce Ukraine ta ki amincewa da wannan tayin.
Prigozhin wanda ya kasance makusancin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, a fili, ya yi barazanar janye mayakansa daga yankin Bakhmut, inda suke kan gaba wajen farmakin da Rasha take kaiwa, har sai dai idan sun samu makaman da suke bukata.
Ya fada a cikin wani sakon cikin sauti cewa, za a dauke shi da mayakansa a matsayin munafikai idan suka kaurace daga yankin.
Jaridar ta The Post, ta ruwaito wannan tayin na Prigozhin ya biyo ta hannun abokan huldarsa da jami’an sirrin Ukraine
Wani mai magana da yawun White House, ya ki ya ce uffan a game da rahoton wanda ya samu asali daga wasu takardun sirrin Amurka da aka fitar a wani dandalin sada zumunta na manhajar Discord.