Bayan nazari akan gajimaren da ya ke fitowa a yankin gabashin arewacin Najeriya, hukumar hasashen yanayi ta kasar NIMET ta fitar da wata sanarwa da zummar zaburar da al’umma a game da yiwuwar samun saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin kwanaki masu zuwa a wasu jihohin arewacin Najeriya.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa ana kyautata zaton su wadadannan gajimaren za su yi gabas da kasar domin samar da yanayin gajimare hade da iska mai karfi tare da ruwan sama a biranen Filato, Abuja, Nassarawa, Jigawa, Adamawa, Yobe, Borno, Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano da Katsina cikin sa’o’I 2-6 masu zuwa.
Hukumar ta NiMET ta kuma yi gargadin cewa; a yankunan da ake tsammmanin haduwar hadiri, akwai kuma yiwuwar saukan ruwan sama wanda yakan na iya kada bishiyoyi ko kuma itatuwan lantarki da kuma abubuwan da ba a killace su ba kana, yana iya rusa gidaje.
A bisa wadannan dalilai ne ya sa hukumar ta bai wa al’umma shawarar a kasance a cikin gidaje musamman ma a lokacin da ake ruwan domin guje wa yiwuwar tsawa ta afka wa mutum.
Baya ga al’umma, NiMET ta gargadi kamfanonin jiragen sama da su tabbata suna bibiyar bayanan yanayi daga lokaci zuwa lokaci daga NiMET domin tsara harkokinsu na jigilar fasinjoji ba tare da wata matsala ba.
Ta kuma yi nuni da cewa, ana iya samun ambaliyar ruwa a sakamakon ruwan sama mai karfi ko kuma matsakaici, sabo da haka ta shawarci al’umma da a dau mataken kariya.
"Kwararru a fannin tunkarar bala’i, hukumomi da daidaikun mutane su kiyaye domin guje wa rasa rayuka da dukiyoyi a wannan lokaci na damuna".
Cibiyar ofishin hukumar NiMET ta bada tabbacin cigaba da bibiyar batun yanayi kana, za ta cigaba da bada bayanai.