Wannan farmakin aka kai da jirage marasa matuka da makaman mizile, su ne farmakin da Rasha ta kai mafi girma cikin watanni 3
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta ce na’urorin kare hare haren saman Rasha sun kakkabo wasu jirage marasa matukan 36 a wasu yankuna a yammacin Rasha cikin sa’o’I 3 kawai a yau Lahadi.
Ma'aikatan lafiya a wani asibiti sun sanar cewa dubban yara suna fama da matsanancin matsalar rashin abinci.
Batun bakin haure ya kasance batu mai mahimmanci a zaben shugaban kasar Amurka na 2024, inda kaso 28% na Amurkawa suka bayyana shi a matsayin babbar matsala a kasar.
Likitocin Isra’ila sun ce wata babbar mota tayi karo da wata motar safa a daura da Tel Aviv, wanda yayi sanadiyyar jikkata mutum 35.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce zata mai da kakkausar martani biyo bayan hasashen cewa Ukraine zata kai mata farmaki da makamai masu cin dogon zango.
Sannan masana sun ce bakin haure sabbin zama 'yan kasa da suka cancanci kada kuri’a zasu iya sauya akalar sakamakon zaben shugaban kasar da za ayi nan da 'yan kwanaki a watan Nuwamba, musamman ma a manyan jihohin raba gardama.
Domin Kari