Amurkawa za su fuskanci matsanancin sanyin mai kama da yanayin Siberia. Wani yanayi mai kadawa tsakanin kuryar duniya a fadin arewacin duniya wanda zai kai ranar bukin rantsar da Trump a wa’adi na biyu ya kasance wanda aka yi cikin yanayi mafi sanyi cikin shekaru 40 a cewar masana yanayi.
Iskar da za ta fara kadawa daga daren Alkhamis daga Arewacin Amurka wadda ake ma ta lakabi da Rockies, zata kada yankin gabashi zuwa yankin kudu mai nisa har zuwa tsibirin Florida cikin ‘yan kwanaki. Kimanin Amurkawa miliyan 280 ne za su fuskanci matsanancin sanyin da ya zarta yanayin sanyin Anchorage, a jihar Alaska inji Masanin kimiyyar yanayi Ryan Maue.
Masanin kimiyyar yanayi Judah Cohen, na cibiyar Atmospheric Environmental Research ya ce “Wannan zai kasance cikin hunturu mafi sanyi da aka fuskanta cikin shekaru 10, zuwa 15”. “Iskar tana kadawa daga Siberia ne. Sannan, wannan yanayi ya dace da sauyin nan domin a duk sa’adda igiyar kuryar duniya ta buda iskar tana tasowa daga Siberia ne sannan ta dire a Amurka.”
Iskar zata karasa Washington gabanin bukin rantsar da Trump a farfajiyar majalisar dokokin Amurka a ranar Litinin. Hukumar yanayi ta kasa ta yi hasashen cewa alkaluman yanayi zai kai digiri 22 wato -6 a ma’aunin Celsius da rana lokacin bukin shan rantsuwar, alkaluma mafi sanyi tun bayan lokacin bukin shan rantsuwar wa’adin aikin shugaba Reagan da alkaluman suka kai digiree 7 wato -14 a ma’uanin Celsius. A lokacin bukin shan ratsuwar Barrack Obama a 2009 kuma, alkaluman sun kai digiree 28 wato -2 a ma’aunin Celsius.
Bugu da kari kuma, hasashen na nuna cewa ma’aunin iskar da zata kada akan 30 -35 ko wani mita cikin sa’a daya wato kilomita 48 -56 a ko wace sa’a.
Dandalin Mu Tattauna