Wani rahoton da kafar labarai ta Reuters ta wallafa, ya ce fitattun mawaka Billie Eilish, da Lady Gaga, da Mitchel da Jelly Roll za su shiga sahun manyan fitatun sunayen da za su hallarci wani gangami da aka shirya yi a karshen watan Janairu a Los Angeles don tallafa ma wadanda ibtila’in wutar daji ta sha inji wadanda suka shirya gangamin.
An lakaba wa gangamin da aka shirya yi don neman tallafin taken FireAid, sauran fitattun da za su hallarci gangamin sun hada da Green Day, Gracie Abrams, Katy Perry, Red Hot Chilli Peppers, Sting da Stevie Nicks. Dave Mathews da John Mayer su ma za su yi waka tare a karon farko.
A ranar 30 ga watan Janairun nan ne gangamin zai gudana a Intuit Dome da Kia Forum a Inglewood, California da ke daura da Los Angeles. Za a nuna gangamin a wasu gidajen majigi na AMC sannan za a yada shi ta kafafen Netflix, Max, Apple Tv, Prime Video, Spotify, YouTube da sauran su.
Wani sashen Los Angeles, birni mafi girma na biyu a Amurka, sannan tungar mawaka da dama, gobarar daji ta yi kacakaca da shi a makon da ya gabata, ta lakume ran mutane 25.
Dandalin Mu Tattauna