Hada hada ya fara kan kama a garin Potiskum, babban birnin kasuwancin jihar Yobe, bayan da yayi fama da tarzomar ‘yan Boko Haram.
Amma babban abun da jama’a, ke kokawa akai shine yadda jami’an tsaro suka rufe manyan hanyoyi na cikin gari duk ko da yadda ake ganinyanzu kam zaman lafiya na kan kama sosai.
A cewar Alhaji Burra Dada na Alhaji Umaru sarkin Kukuri, rurrufe hanyoyin nan ya shafi shaguna masu yawan gaske, yana mai cewa ba zai kasa shaguna dari biyu da hamsin ba, kaga wadannan shaguna Allah, yasan yawan miliyoyinkudin da ake rasawa kuma tattalin arzikin da ya shafa bisa yadda abubuwa suke tafiya idan ka duba da yadda kasuwanci da wasu mutanen dake cin moriyar ga yadda yanzu ya zama, bad an kasuwan da ba bashi ake bin sa ba kuma duk a sanadin wannan alamari ne.
Zazzabin tarzomar Boko Haram, din na ci gaba da kassara tattalin arzikin garin na Potiskum, wanda ke daya daga cikin manyan garuruwa dake arewacin Najeriya.
Wakilin muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, da ya zaga sassa da dama a cikin garin ya ganewa idon sa irin ta’annatin da ‘yan Boko Haram, suka yiwa bankuna a gari, yayin da wasu suka riufe dan ra’ayin kansu domin dalilin tsaro, abunda yasa mutanen garin ke tafiya jihohi kamar Gombe, Bauchi, Kano da Jigawa, domin gudanar da hada hadar Banki.
Your browser doesn’t support HTML5