Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: Kudin Wasu Maniyatta Ya Yi Layin Zana


Hajj
Hajj

Wasu maniyatta da dama a jihar Filato ba zasu samu saukar da farali ba bana saboda bacewar kudaden da suka biya na tafiya

Hukumar alhazan jihar ta kuduri yin bincike kan kudin wasu maniyatta 406 wanda ya haura nera miliyan 260 da yanzu suka yi layin zana.

Binciken da Muryar Amurka ta gudanar a hukumar ya nuna cewa shekaru da dama wata al'ada ce a hukumar ba duka wadanda suka biya kudin zuwa hajji suke samun yin tafiyar walau a ce mutum ya biya a wurin da bai dace ba ko kuma wani yayi dabara ya wawure kudin maniyattan,

Wasu da suka biya kudin amma basu samu shiga jerin sunayen wadanda zasu tafi ba sun shaida cewa wasu sun biya a banki ne wasu kuma sun ba jami'an hukumar ne.

Wata tace tun bara suka biya kudin amma jami'an hukumar basu yi masu komi ba saidai su dinga turasu nan ko can. Wasu suna rike da takardun shaidar biyan kudaden.

Jami'an hukumar suna koran mutanen saboda sun nemi a mayar masu da kudadensu. Shugabansu yace gasu su 406 an kusa kammala shirin zuwa hajji amma basu ji komi ba.

To saidai gwamnan jihar ya umurci hukumar ta ba mutanen sauran kujeru 30 da suka rage a kuma basu hakuri da alkawarin yin bincike da zara an dawo daga hajji.Bayan bincike idan ta kama za'a mayarwa mutane kudadensu ko kuma su jira shekara mai zuwa.

Sakataren hukumar Danlami Muhammad yace da idan mutum ya zo da takardar biyan kudi sai a bari ya hau jirgi lamarin da yasa ana samun hawa hawar mutane. Sai a ce alhazai 1500 zasu tafi amma ranar tafiya sai su daura 2000. Wai da ma'aikaci sai ya yankawa 'yanuwansa tikiti ba tare da biyan kudi ba. Yace yanzu ba haka ba ne.

Yanzu sun sa doka suna kuma bincikawa kafin a ba mutum kujera. Duk wanda zai tafi hajji sai ya je banki ya biya kana ya kawo shaida.

Hukumar ta yanzu zata yi cikakken bincike. Duk wanda ya biya zata gayawa gwamnati ta bari ya tafi aikin hajji amma ta bi wadanda suka wawure kudaden ta karbo daga hannunsu.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG