Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Ya Kamata Matar Shugabn Kasa Ta Kafa Nata Ofishin


Hajiya Aisha Buhari matar shugaba Muhammad Buhari
Hajiya Aisha Buhari matar shugaba Muhammad Buhari

An dade ana kai ruwa rana akan batun ofishin matar shugaban kasa inda wasu suna ganin bai dace ba saboda bashi cikin kundun tsarin mulkin kasar

Wani lauya Yakubu Sale Bawa yace ofishin matar shugaban kasa ko gwamnan jiha baya cikin tsarin mulkin kasa.

Masu sharhi sun ce galibi ana anfani da ofishin wajen bannatar da dukiyoyin jama'a wala a gwamnatin tarayya ko na jihohi. Lamarin ma har ya kaiga kananan hukumomi.

Akan wannan maganar mai magana da yawun fadar gwamnatin Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana matsayin shugaba Muhammad Buhari.Shugaban bai amince da ofishin "First Lady" ba. Ba ma sunan ba duk wani abun da doka bata yadda dashi ba ba zai karba ba.

Tunda babu shi a tsarin mulki shugaban kasa yayi alkawari ba za'a gudanar dashi ba.

Can baya akan ga matar shugaban kasa ko gwamna cikin tirkatirkan motoci da jerin gwano da jiniya. Ban da haka har ma ana nada masu ma'aikata wadanda da ake biyansu da kudin talakawa.

Kundun tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ofishin shugaban kasa da na mataimakinsa sai kuma na gwamna shi ma da mataimakinsa.

To saidai wata tsohuwar 'yar majalisar tarayya ta goyi bayan ofishin tana cewa idan an haramta wato an cire mata daga harakar gwamnati ke nan domin babu wanda zai kula dasu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG