Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faduwar Hannun Jari a Kasar Sin Ya Rutsa da Kasuwannin Asiya


Mutane na kallon yadda hannun jari ke faduwa
Mutane na kallon yadda hannun jari ke faduwa

Darajar hannayen jira a kasar Sin sun jagoranci ragowar kasuwannin hannayen jari a nahiyar Asiya kara faduwa yau Talata, inda suka yi kasa da kaso 7.6 cikin 100.

Darajar manyan alkaluman hannayen jari na Shanghai sun fadi biyo bayan bude kasuwar, sannan a wani lokaci sun farfado da kaso 4 cikin dari. Amma hannayen jarin sun kara faduwa yau da rana. Kasuwanin jari a kasar Japan da yankin Hong Kong duk da cewa sun samu dan cigaba, to suma masu hada-hada sai sayar da hannayen jarin su kawai suke yi.

Alkaluman Nikkei na kasar Japan sun rufe da faduwar kaso 4 cikin dari, sannan alkaluman Hang Seng na Hong Kong su kuma sun yunkura da ‘yar riba kadan sa’o’i kafin rufe kasuwar.

A halin da ake ciki kuma, alkaluman hannayen jari a Britaniya, Jamus da Faransa duk sun kara daraja da kaso 2 cikin dari kafin kasuwannin su yi nisa yau Talata.

Fargaba saboda tsaikon bunkasar tattalin arzikin kasar Chana ya tunzura faduwar darajar hannayen jari a duk kasuwannin duniya, da ma faduwar farashin danyen mai yau Talata tun jiya Litinin.

XS
SM
MD
LG