Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) Karo Na 55


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Ga dukkan alamu kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na taronta na karo na 55 a daidai lokacin da ake matukar bukatar gudunmowarta, ganin kasar na kokarin ganin bayan masu cin hanci da rashawa da kan samu daurin gindin wasu ma'abuta shari'a.

Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA, a takaice), ta fara taronta na karo na 55, wanda za ta yi kwanaki 6 ta na yi, a daidai lokacin da Najeriya ke bukatar gudunmowar kowane bangare ciki har da na lauyoyin. Wata kila shi ya sa ma bana ta zabi taken, “Lauyoyi Da Cigaban Kasa.”

Hasalima Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci su taimaka wajen yakin da ake yi da miyagu kuma kar su basu mafaka a tsarin aikinsu. Da ya ke bayani a hirar da su ka yi da abokin aikinmu Sahabo Imam Aliyu, wani jigon kungiyar mai suna Barrister Hassan Liman y ace a mafiya yawan kasashe lauyoyi ke tasiri wajen kafa doka.

Don haka da Sahabo ya kawo batun kiran da Shugaba Buhari ya yi na su taimaka wajen dakile miyagu sai y ace ai dama aikin da aka rantsar da su akai Kenan. Ya ce Shugaba Buhari mutum ne da aka sani da bin doka da oda, wanda kuma ke matukar kyamar cin hanci da rashawa don haka za su ba shi hadin kai.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG