Dauke da tutoci masu launin ja da fari, alamar nuna adawa, masu zanga zangar sun yi cincirindo a zagayen gidan shugaba Lukashenko suna kuma fuskantar jami’an tsaro dauke da makamai, suna kuma tsaye a gaban motocin gidan yari da mesar ruwa.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce an kame akalla masu zanga zanga 140 a jiya Lahadi kafin su tarwatsa cikin lumana.
Alexander Lukashenko, wanda ya cika shekaru 66 a jiya lahadi, ya yi shekaru 26 yana mulki, a ranar 9 ga watan Agusta aka sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zabe da ake zargi na cike da magudi, zargin da ya musanta.
Babbar 'yar takara a jam’iyar adawa Sviatlana Tsikhanouskaya, ta ce sam bata amince da sakamakon zaben ba. Ta bar kasar zuwa Lithuania saboda abinda ta bayyana da kare lafiyar ‘ya ‘yanta.