Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Huldar Isira'ila Da Hadaddiyar Daular Larabawa Na Dada Kankama


Yarima Mai Jiran Gado Sheikh Moh'd bin Zayed Al-Nahyan, Shugaba Donald Trump da kuma Firaminista Netanyahu.
Yarima Mai Jiran Gado Sheikh Moh'd bin Zayed Al-Nahyan, Shugaba Donald Trump da kuma Firaminista Netanyahu.

Idan komai ya gudana kamar yadda aka tsara, za a yi bukin rattaba hannu tsakanin Isira'ila da Hadaddiyar Daular Laraba watan gobe a birnin Washington D.C.

Kasar Isira’ila na fatan yin liyafar rattaba hannu a birnin Washington DC zuwa tsakiyar watan Satumba, saboda yarjajjeniyar da ta cimma da Hadaddiyar Daular Larabawa, Wani babban jami’in gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu ne ya fadi haka yau dinnan Lahadi.

Shugaban Amurka Donald Trump da manyan hadiman Netanyahu, za su tsai da ranar rattaba hannun, lokacin da jami’an na Isira’ila su ka isa Abu Dhabi gobe Litini don tattaunawa, abin da Ministan Harkokin Hadin Kan Yanki, Ofir Akunis ya fada kenan.

Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, president of UAE
Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, president of UAE

Babban Mai Bai Wa Trump Shawara, Jared Kushner da wasu wakilan Amurka za su isa Isira’ila a yau dinnan lahadi don shirya tafiya Hadaddiyar Daular Larabawa din.

Akunis ya kara da cewa gwamnatin Netanyahu na fatan hidimar rattaba hannun, za ta auku gabanin abin da ya kira, “Rosh Hashanah dinmu,” wato sabuwar shekarar Yahudu, wadda ta yi daidai da ranar 18 ga watan Satumba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG