Wannan ranar ta Hausa ta samo asali ne bayan da wasu matasa 'yan Najeriya a shafukan sada zumunta suka ayyana kowace ranar 26 ga watan Agusta a matsayin ranar da za a karrama harshen Hausa domin bunkasa yaren.
Muhimmancin harshen Hausa a Nijar da yadda Hausa ke matsayin wata hanyar sadarwa a tsakanin al’ummar wannan kasa da takwarorinsu na sassan duniya ya sa kwararu da shuwagabanin kungiyoyin marubuta da na bunkasa al’adun Hausa shirya wata mahawarar bainar jama’a.
An kuma baje kolin litattafan Hausa da nufin karrama ranar ta Hausa.
Bikin na Ranar Hausa karo na 5 ya sami halartar wata tawagar marabuta da masu yada harshen hausa ta kafafen sada zumunta daga tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin Kabir Ahmed S Kouka.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun yi na’am da wannan tsari domin a cewar Iro Abdoulaye, jami’i a ma’aikatar ilimi da bunkasa harsunan gida a Nijer "abu ne da yayi dai dai da manufofin gwamnatin kasar."
A shekarar 2015 ne aka ayyana ranar 26 ga watan Agusta a matsayin ranar hausa ta duniya bayan da bincike ya tabbatar da gudunmuwar da harshen hausa ke bayarwa a harkokin sadarwa a tsakanin al’umomin duniya a fannoni daban-daban musamman a wannan lokaci da hankali ya karkata wajen kafafen sada zumunta na zamani.
Ga Suleiman Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum