Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Wani Bututun Mai a Syria Ta Yi Sanadin Daukewar Wutar Lantarki


Wata fashewa akan wani bututun mai a Syria ta yi sanadiyyar daukewar wutar lantarki tsawon daren jiya.

Kafar yada labaran kasar ta nuna hotunan wuta na ci a yau Litinin abinda jami’ai suka ce an gani a kusa da Damascus babban birnin kasar.

Ministan man kasar ya ce da farko an ga alamun kamar ta yiwu harin ‘yan ta’adda ne ya haddasa fashewar.

Kafar yada labaran SANA ta ambaci ministan wutar lantarkin kasar ya na cewa an fara maido da wuta a wasu lardunan kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG