Yanzu haka dai an kwana ana zanga-zanga a garin na Milwukee, wanda yayi dalilin kona shaguna 6, kana aka kona motocin ‘yan sanda, yayin da aka jiwa wata ‘yar yarinya rauni, haka kuma wasu jami'an ‘yan sanda da dama sun samu rauni ciki ko har da wani bawan Allah da ya fita hayyacin sa sakamakon buga kansa da akayi akan kankare.
Yanzu haka dai an tsare mutane 17 sakamakon wannan rikicin.
Barrett dai ya yaba wa ‘yan sandan garin na Milwaukee, abin da ya kira tsananin kokarin nuna hangen nesa da suka nuna sakamakon wannan tashin hankali, ya shaidawa manema labarai cewa har tsawon wannan tarzomar ‘yan sanda basu tunzura ba, balle har suyi harbi ko sau daya har tsawon daren asabar din da aka kwashe ana zanga-zangar.
Kana ya roki iyaye da kar su bar ‘ya’yan su su kasance guraren da ake zanga-zangar, kuma yace yana iya kafa dokar hana fita idan bukatar hakan ta taso.
Babban shugaban ‘yan sanda na garin Miwaukee Edward Flynn, ya bayyana dan talikin da aka harba a daren asabar din da ya haifar da tarzoma da cewa sunan sa Sylville Smith, dan shekaru 23 da haihuwa, yana da tarihin yawan tsarewa da aka yi masa lokutan baya.