Shugabar 'yan Democrats a Majalisar Wakilan AMurka Nancy Pelosi, jiya Asabar ta yi gargadi ga sauran 'yan jam'iyyarsu ta Democrats da ke Majalisar, cewa su daina ansa waya ko kuma bude duk wani sakon "email," bayan da ta gamu da, abin da ta bayyana da kiraye-kiraye da sakonnin "batsa da shirme," biyo bayan kwarmata bayanan da su ka shafi 'yan Majalisar wajen 200 da wani wanda ya kutsa cikin wasikunsu na yanar 'internet' ya yi.
Wani mai kutsen na'urar kwamfuta, wanda ya bayyana sunansa da Guccifer 2.0, ya bayyana a yanar internet cewa ya kaddamar da kutse har sau biyu kan bayanan kungiyoyin jam'iyyar ta Democrat da ke yanar internet - wato da fallasa bayanan mutane da kuma musayar sakonnin tsakanin shugabannin jam'iyyar ta Democrat a watan jiya.
Mai kutsen ya sabunta shafukansa da ke dandalin Wordpress.com ranar Jumma'a, inda ya bayyana adiresoshhin email, da lambobin waya, da kuma adiresoshin gidaje da kuma sauran bayanan 'yan Majalisar.
Shuagabar 'yan Democrats a Majalisar Wakilan ta ce za ta canza lambobin wayarta, kuma ta shawarci koya ya yi hakan.