Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Sama Bai Hana Zanga Zanga Ba A Kasar Philippines


Masu zanga zanga a kasar Philippines
Masu zanga zanga a kasar Philippines

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka kasance cikin ruwan sama a babban birnin Phillippine jiya Lahadi, domin kawai su nuna rashin amincewar su da yunkurin da shugaba Rodrigo Duterte, ya keyi na ganin an karrama tsohon shugaban kasar Ferdinand Marco wajen yi masa jana'izar ban girma.

bayan babban birnin jihar, haka kuma an gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar kan nuna wannan kyamar, amma kuma shugaba Duterte ya tsaya kai da fata cewa zai dauko gawar tsohon shugaban kasar daga garin su na haihuwa zuwa kabarin da ake binne jan gwarzaye na kasar dake Manilla, kuma zai yi hakan ne a cikin watan gobe.

Sanata Risa Hantiveros, wadda ta shiga cikin sahun masu zanga-zangar tace Marcos ya shiga kundin tarihi a matsayin wanda bai yi nadama ba a matsayin makiyin fitattun mutanen kasar, don haka tana kira ga shugaba Duterte da kar ya yarda ya gwabza wannan babban kuskuren da yake kokarin tafkawa.

Wasu daga cikin masu gudanar da wannan zanga-zangar ko sun hada da wadanda suka sha hukuba gidan yari lokacin da aka tsare su zamanin mulkin marigayin Marco.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG